Daren Farko

Daren Farko
Daren Farko


Daren farko dai wani muhimmin dare ne a rayuwar sabbin ma’aurata. Dare ne wanda wadannan ma’aurata kan san juna ciki da waje [ta hanyar jima’i], su kuma fahimci wasu abubuwa game da juna.

Dare ne wanda ango ke fara tarawa da amaryarsa, bayan sun gudanar da wadansu aiyuka [na addini, da na gargajiya]. A kuma daren ne zai fahimci wacce irin mace ya aura. Shin budurwa ce cikakkiya, ko kuwa dai sakan-hand ce a siffar budurwa.

Akwai tarin sarkakiyoyi a cikin kwakwalen mata [musamman wadanda ba su taba zina ba] game da wannan daren. Sau tarin lokuta sai ka ji ana tsorata su, ana jiyo musu irin azabar da za su dandana a hannun mazajensu a wannan daren.

{toc} $title={Abubuwan Da Ke Ciki}

Abin da ke sanya ni takaici shi ne; masu borata ‘yammatan mafi akasarinsu ‘yan‘uwansu mata ne wadanda su ka taba aure ko su ke zaman aure.

Ko ma dai menene, daren farko, dare ne mai dauke da ni’imomi masu tarin yawa ga ma’aurata domin daga shi ake samun cikakkiyar yarda [ta rashin zina] tsakanin ango da amaryarsa.

Yayin da mutum ke bincike game da daren farko a yanar gizo-gizo, na tabbata zai ci karo da wadannan abubuwan da zan yi bayani a kansu a kasa. Saboda haka zan yi bayani a kansu kafin mu cigaba da abin da ya hada mu a wurin nan.

A Daren Farko – Hausa Series Film by Nazifi Asnanic

Shirin nan mai dogon zango (Series) wanda tsohon fitaccen mawakin nan na Nazifi Asnanic ke daukar nauyi karkashin kamfaninsa mai suna Asnanic Movie Tone

Ana kuma haska shi ne a tashar YouTube mai suna Nazifi Asnanic. Ga masu sha’awar kallonsa sai su garzaya tashar domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Game da Shirin

Shiri ne wanda baki daya ke dauke da hardaddiyar cakwakiya game da daren farkon wasu ma’aurata.

Sannan Season One yana dauke da eposides 14, yayin da a halin yanzu su ke kan yin Season 2, kuma sun dakata ne a episode 5.

Masu kallon wannan shiri Season 2 episode 6 su ke jira amma abin da ke da daure kai shi ne yadda yau wajen watanni 2 kenan ba tare da an dora cigaban fim din ba.

Ga dukkan alamu dai sun daina.

A Daren Farko – Hausa Novel by Husna Gimbiya

Shi kuwa littafin soyayya mai suna “A Daren Farko” marubuciya Husna Gimbiya ce ta rubuta shi.

Kamar yadda marubuciyarsa ta bayyana, littafi ne da ke dauke da labari wanda ke dauke da darussan rayuwa a soyayya da kuma sauran al’amura na kaddara.

Duba da irin yadda makaranta su ka yabi salon labarin, hakan ya nuna cewa littafin zai yi dadin karatu. 

A murfin littafin, ga abinda marubuciyar ta fara da shi, “Shin me murfin ke lullube da shi? Makaranci kadai ke da damar bude sirrin da ke rufe cikin murfin.”

Za ku iya karanta littafin nan mai suna ‘A Daren Farko’ ta hanyar shiga shafin Bakandamiya.com ko kuma ku yi wa Husna Gimbiya magana a shafukan sada zumunta domin sayen kwafinku.

A Daren Farko – Hausa Song

Waka ce ta soyayya wacce mawaki Umar M. Sharif ya rera ta, duk wanda bukatarsa ita ce ya saurari wannan waka wacce Umar ya yi, to, a shawarce ya tafi Mdundo, Audiomack, Spotify, Boomplay, ko Apple Music domin ya saurareta.

Ko kuma ya neme ta a yanar gizo ta hanyar rubuta “mp3 download” a karshen title din wakar da sunan mawakin. Ko kuma ya gwada yin irin wannan salon, “Umar M. Sharif – Daren Farko Mp3 Download” daga nan sai ya shiga shafin da ya ga sun nuna masa akwai wakar sun dora, sannan sai ya sauke ta.

Shirye-shiryen Daren Farko

Kasancewarsa dare mafi muhimmanci a rayuwar ma’aurata, shi yasa yana da kyau daga ango har amarya su yi wadansu ‘yan shirye-shirye kafin zuwan wannan daren saboda daga wannan dare ake darsa ginshikin zaman rayuwar aure tsakanin ango da amarya.

Daga cikin shirin da za ku yi kafin zuwan daren auren akwai:

Niyya Mai Kyau

A cikin Arba'una Hadith, an ruwaito cewa Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su Kara Tabbata a Gareshi) ya ce, “Hakika aiki ba ya yiwuwa sai da niyya.”

Niyya ita ce abar da ya kamata amarya da ango su fara tsarkakewa tukunna, su kyautata niyyarsu da nufin samun alkhairi da albarka daga aurensu. 

Duk irin niyyar da ku ka kullata gabanin aurenku, to, irin sakamakon da za ku samu kenan [in hairan, hairan, in sharran, sharran] bayan auren.

Babban dalilin da yasa ake yin aure ba don namiji da mace su samu damar biyan bukatunsu na jima’i ba ne [kare kai daga zina da dangoginta] kadai, ana yin aure ne don samun abokiyar rayuwa, uwar ‘ya‘ya, kuma a lokuta da dama abokiyar shawara.

Kuskure ne gareku ku kudurci yin aure saboda tsananin soyayyar da ke tsakaninku ba tare da yarda da cewa za ku yi hakuri da juna ba kuma bautar Allah za ku yi.

Kada kuma ku yi niyyar yin auren domin kyau [jiki], ko dukiya, ko matsayi kadai ba tare da kun saka Allah a cikin lamarinku ba ta hanyar tsarkake niyyarku.

In har ango da amarya su ka kudurci niyyar yin aure saboda Allah, sai Allah Madaukakin Sarki ya dubi zuciyarsu ya shiga cikin lamarinsu, ya sanya wa abin albarka, su yi rayuwar aure mai tsabta abar sha'awa ga sauran mutane.

Kawar da Kunya

Ga wadda bai taba jima’i ba [musamman mata] dole za a ji fargaba [kamar tsoron ciwo saboda razanarwa da ake yi musu kafin auren] da kuma kunyar fara shi.

Haka su kansu mazan ma akwai wadanda ke tsoro da fargabar zuwan daren musamman samari [baki a tarawa da mace].

In har kuna da bukatar yin cikakkiyar nasara a darenku na farko, to, dole tun kafin aurenku sai kun ‘dan rage jin kunyar kin tattaunawa akan yadda darenku na farko zai kasance.

Ta haka, sai ku samu damar fahimtar wadansu abubuwa da dama game da auren tun kafin lokacin auren [amma fa hakan ba shi ya ba ku damar yin zina kafin auren ba].

Sannan yana da kyau ku nemi litattafai da ke bayani akan jima’i da ma yadda za a tunkari amarya a daren farko domin samun wadataccen ilimi akan abin da ku ke kokarin tsoma kafarku a ciki.

Jawabi na, “Za ku iya yi mana kallon ‘yan iska [wato masu bibiyar tsangayoyin nan] amma kuma muna karuwa fiye da yadda ku ke zato. 

“Akwai wasu tsangayoyi da kuma mutane masu bayani akan jima'i da rayuwar aure har ma da shawarwari da ya kamata ku rinka bibiya domin samun ilimi a sahar kafin ku shiga. 

“Daga cikinsu akwai su Tsangayar Malam Tonga, Ustaz Usman, Muneerat Abdussalam da sauransu. 

“Kai wasu lokutan ma ba laifi ba ne in har ku ka kalli fim din batsa domin fahimtar yadda ake gudanar da jima’i [sai dai ku yi sani cewa: kaso 90 na abubuwan da ke ciki duk shiri ne, akwai darakta, furodusa, masu samar da location da sauransu wajen daukar wadannan bidiyon, don haka kada ku yi tunanin abin na zahiri ne, kawai drama ce, amma za ku samu ilimi sosai. 

Kuma kada ku cika yawan kallonsu domin suna da illa kwarai da gaske. Sannan ba komai na ciki ake gwadawa ba kamar namiji ya sa bakinsa a farjin mace –baki wuri ne na ambaton Allah– saduwa da mace ta baya dss.

Bugu-da-kari, haramun ne ga musulmi ya rinka kallon tsiraicin ‘dan‘uwansa musulmi ko ma ba musulmi ba. In har ku ka kiyaye idanuwanku daga kallon finafinai masu bayyana tsiraicin mutane, to, Allah zai kiyaye tsairicinku.

Sannan su kansu rubututtuka na batsa, haramun ne a musulunci mutum ya rinka karantsu. Don haka sai mu kiyaya].”

Addu'ar Daren Farko

A darenku na farko, ango, ka yi wa Allah kada ka haike wa amaryarka kamar wani ‘dan akuya. Ka rinka bi a sannu a hankali wurin takalar amaryarka da zance bayan kun saki jiki da juna sai ka umarceta da ta yi alwala domin ku yi Sallah Raka’a biyu ku yi wa Allah godiya.

Bayan kun sallame, sai ka juyo, ka dafa goshinta ka yi muku addu’o’i iyaka iyawarka, amma fa kara da wannan wacce Manzon Allah (S.A.W.) ya umarta da a yi.

Ka ce, “Allahumma inni as'aluka min khairina, wa khairi ma jabaltaha alayya, wa a'uzubika min sharrina, wa sharri ma jabaltaha alayya.”

In kuma ba ka iya da larabci a Latin ba, sai ka karanta da Hausa, ga ta nan kamar haka, “Ya Allah ina rokonta alkhairan da yake tattare da ita, da alkhairan abinda ka dorata akai na da shi, kuma ina neman tsarinka da sharrin da ke tattare da ita, da kuma sharrin abin da ka dorata a kaina da shi.”

Daga nan sai ku ci abin da ku ka tanada, sai ku kwanta, amma kafin haka, ka fara janta da hira har ta saki jiki da kai tukunna. Kuma ko wani abu za ka yi mata, to, ka far a sannu har sai ka fahimci ta saki jiki da kai tukunna.

Sannan, ko tarawa za ka yi da ita, ka yi a sannu, ka kuma nuna mata kana tausanta in har ka ji yanayinta kamar kuka ko wani abu haka.

Shirya Jiki

Yana da kyau amarya da ango su shirya jikinsu kafin zuwan darensu na farko amma zan so ku san wani abu kafin ku kai ga yin hakan.

Ga ango: Kada ka yi tunanin a darenku na farko ya zame maka wajibi ka sha maganin kara karfin maza wanda ake talla domin in har ka sabarwa da matarka muddin za ka tara da ita sai ka sha magani to da haka za ta tafi.

Ka nemi maganin gyaran ciki da mara ka sha, sannan ka rinka cin abinci masu kyau da gyaran jiki, kana kuma motsa jiki domin samun wadataccen kuzari.

Ga amarya: Ba laifi ba ne a tsuma ki, a shirya ki, a yi miki gyaran fata da sauransu. Amma ki yi sani cewa, in dai ba dama can mazinaciya ba ce ke, to ba kya da bukatar duk wani hadi wanda ya danganci matsi yayin shirye-shiryenku na farko. 

In kuwa sakan-hand ce, to, ba laifi ba ne don kin nemi hadin matsin gaba domin mijin da za ki aura ya yi tunanin budurwace ke. Haka kuma zamani ya ci gaba, akwai ma wanu element da ake siya mata ke amfani da shi domin dawo da budurcinsu na jabu a daren farko.

Yin amfani da duk wani abu da ya danganci matsin gaba, ga budurwa, ita zai cutar yayin tarawarta da namiji don haka sai a kiyaye.

Ko ma dai menene; yana da kyau ku shirya jikinku kafin darenku na farko. Zabin abin da za ku yi yana gareku.

Kyakkyawan Zato

An zo wurin da na dade ina jira.

Maza yana da kyau ku yi wa amarenku kyakkyawan zato musamman game da zargin zina saboda kun ji murfin budurcinsu a balle ya ke. 

Ku yi sani cewa, ba fa sai a iya yin jima'i ake iya samun akasin ballewar murfin budurci ba.

Akwai abubuwa da dama da ke sa a rasa murfin budurci kamar su;

  1. Hawa keke
  2. Gudu
  3. Wasanni (kwallo, tsale-tsalle dss)
  4. Hawa doki ko jaki 
  5. Sa yatsa a cikin gaba
  6. Da sauran abubuwan da ka sanya kafofin mace su tale.

Bisa wannan dalili, zan so ku kyautata zato ga amarenku in har ku ka ji murfin budurcinsu ya balle. 

Hakika ba kowacce mace ba ce mazinaciya. Sannan su ma kansu mazan, ba kowanne ba ne mazinaci.

Rashin kyakkyawan zato tsakanin ma'aurata kan sa aure ya ki yin dogon zango, domin hankalin namiji ba zai taba kwanciya da matarsa ba, sannan ita ma hankalinta ba zai taba kwanciya da shi ba.

A nan mu ka kawo karshen jawabinmu akan daren farko, yanzu kuma za mu amsa wadansu tambayoyi ne game da daren farko.

********************************************************************

Saduwar Daren Farko

Ita dai saduwar daren farko ita ce wacce ango ke yi da amaryarsa, kuma ba lallai ba ne dole sai ya yi ta a daren da aka kawo masa amaryar tasa.

In har daga shi har amaryar sun gama gajiya sakamakon hidindimun biki, za su iya hakura sai kashegari sai ya tara da matarsa a duk lokacin da ya ke so [ita ma take so].

Tsakanin miji da mata, babu wani adadi da aka kayyade na saduwar da za su yi kullum tun daga daren farkonsu har zuwa lokacin da rai zai yi halinsa ko kuma su rabu.

Saboda haka kada ki dauka da zafi, ki bai wa angonki hadin kai ku ci amarcinku cikin salama.

Daga lokacin da ku ka saba da tarawar, shi kenan ta zama jiki a gareku, kuma ba za ku na jin kunyar juna ba.

Kuka a Daren Farko

Yin kuka a daren farko ba farilla ba ne, ba kuma bidi'a ba ne, ya danganta da yanayin mace. In kin so za ki iya yi, in kin so za ki iya kin yi.

Amma da wuya in dai budurwa ce ke ba ki ji 'dan zafi ba yayin da angonki ke ya raba ki da budurcinki.

A wannan lokacin, a shawarce, ki shagwabance ki yi masa kuka [amma fa ba raki ba] kuka dai sama sama marar sauti sosai.

Karin wani abu: maza na son mata masu shagwaba musamman yayin da suke tarawa da su, don haka babu laifi in ki yi kukanki ko ma wanne iri ne, walau na dadi, na shagwaba, ko na wahala.

Zabi yana gareki, sai ki zabi wanda za ki yi.

Azabar Daren Farko

Duk inda ka ji ance Azaba, to, azaba ce. Muna kuma rokon Allah da ya raba mu da azaba ko wacce iri ce.

Batun azabar daren farko kuwa, ya danganta da mace.

Dalilin da yasa nace ya danganta da mace shi ne; akwai mata masu shegen raki, ko yaya su ka ji bakon lamari sai su shagwabe, to, irin wadannan in ka ji sun ambaci azabar daren farko to ba mamaki ba ne.

Sannan akwai mata wadanda ba komai su ke yi wa raki ba, sai dai in bala'i ne ya kai bala'i. In har fatar budurcinki na tare da ke, dole kafin ango ya samu damar tarawa da ke sai fatar ta farke, kuma ita wannan fata ba wani kauri ne da ita ba.

Saboda haka ciwon da za ki ji ba wani mai yawa ba ne, sai dai in shegen raki gareki, wannan kuwa kya ce azaba ya gana miki.

Sannan akwai mata wadanda su ba ma sa kukan a darensu na farko, sai dai su yi 'yar kwalla, su wadannan su ne jarumai a cikin amare.

Dadin-dadawa, yin kuka a daren farko ko kuma jin azaba ya danganta da irin angon mace, in har angonki ya karanci tarawa da budurwa, to, komai zai yi miki shi ne sannu a hankali har a kai ga nasara ba tare da kin sha wata bakar wahala [azaba] ba.

Batun azaba a daren farko, ba wata azaba ba ce, 'dan zafi ne kawai mace za ta ji. Amma in kun ji ta ce azaba, to, dama can raguwa ce. Kuma jin azabar ya danganta da ango, in zuwar mata ya yi kamar wata dabba, to, zai iya ji mata rauni, amma in a sannu a hankali ya je wa amaryarsa ba batun wata azaba.

Kammalawa

Alhamdulillah. Na tabbata zuwa yanzu wadanda su ka iya jure karanta doron rubutun nan sun yi, wadanda su ka gudu ma sun gudu.

A nan na ke son dasa aya, da fatan Allah ya sa rubutun nan ya amfani mutanenmu, Allah kuma ya gafarta mini kurakuran da na tabka a cikin wannan rubutu.

Allah ka kara wa Annabi (S.A.W.) daraja.

Post a Comment

Previous Post Next Post