Menene Ma'anar Jimla, Misalan Jimla, da Ire-iren Jimla a Hausa

Jimla


Ina yi muku barka da zuwa shafin nan mai albarka.

Yau, za mu tattauna akan jimla, menene ma’anar jimla, har ma da ire-irenta domin daliban ilimi.

“Ita dai jimla jeri ne na kalmomi wadda ke dauke da cikakkiyar ma’ana.”

Kuma babu wanda ya kayyade ya adadin jerin wadannan kalmomin da suka bayar da jimla za su kasance.

In dai za su bayar da ma’ana, to sun bayar da jimla.

Misalan Jima

  • Yaro ya shiga gida
  • Ladidi tana shara
  • Daki ya fadi
  • Tukunya ta fashe
  • Musa ya zo

Ko-da-ya-ke mun kawo ma’anar jimla, amma ba mu kawo ire-iren jimla ba, saboda haka su ma gasu nan a kasa.

Ire-iren Jimla

  1. Jimla Sassauka
  2. Jimla Hardaddiya
  3. Jimla Mai Goyo
  4. Da Jimla Sarkakakkiya

Kammalawa

Za mu dakata a nan, sai kuma a wani darasin na gaba, za ku ji mu da warwararren bayan akan ire-iren jimla har ma da misalansu.

Kada ku manta, yau, mun yi bayani ne akan jimla, misalanta da ire-irenta.

Post a Comment

Previous Post Next Post