Hanyar Samun Kudi ta Online: Ga Guda Shida Mun Kawo Muku

Samun Kudi


Yanzu haka muna cikin karni na 21 wanda ya zo da wadansu sauye-sauye masu tarin yawa a rayuwarmu da ma duniya baki daya. Ciki har da hanyoyin da mutane ke bi wajen neman kudi.

Kusan kowanne mutum na bukatar samun sauki a rayuwarsa. Ba kuma iya bangaren neman kudi ba, a kowanne bangare na rayuwar yau da kullum ma dai mutum na bukatar sauki.

{toc}

Haka kuma nema ya zame wa kowanne taliki [ko talika] wajibi domin ya samu tsira da mutuncin kansa ya kuma biya wa kansa dukkanin bukatun da ya ke da su cikin sauki.

Bisa wannan dalili, ba na da dalilin da zan ga laifinka saboda kana son sanin hanyar da ake bi wajen neman kudi ta yanar gizo [online].

***

Neman Kudi Online

Kusan komai da ku ka sani akwai ma’anarsa, sannan daga ma’anar nan ta sa ake iya gane me ya ke nufi ko me ya kunsa.

Neman kudi ta yanar gizo ma ba a barshi ba baya ba:

“Neman kudi ta yanar gizo dai na nufin yin aiki ta intanit, sayar da kaya, ko gudanar da wani nau’in aiki kullum da nau’ra [walau waya ko kwamfiyuta] da zummar samun kudi.”

Hanyoyin Neman Kudi Online

A gaskiya ba zan iya bugar kirji na zayyano muku duk hanyoyin da ake bi wurin samun kudi a yanar gizo ba. Amma dai zan zabo muku masu gwabi kamar guda shida zuwa bakwai na yi muku bayani a kansu. 

Ga su nan kamar haka:

1. Bude shafin kasuwanci 

Shagunan saye-da-sayarwa ba a iya sararin Allah (wato kasuwanninmu na gida unguwanni) suka tsaya ba. A duniyar yanar gizo ma ana iya bude shagon siyar da kayayyaki iri dabam-daban har ma a kawo wa mutum su har gida.

Za ku iya samun kudi in har ku ka bude shafin e-Commerce ku ka dora kayayyaki mutane su ka yi oda su ka biya kudin ta banki, sai ku aike musu da shi har garin da suke.

Mutane da dama sun yi arziki dalilin irin wannan kasuwanci, kuma shi gudanar da shafin saye-da-sayarwa yana da bukatar a yi shiri na gaske kafin a fara shi, domin sai mutum ya fara nemo irin nau’in kayan da ya ke son sayarwa sannan ya yi odarsu daga wurin vendor dinsa shi ma ya sa su a kasuwa.

2. Yin kwadago a yanar gizo

Yin kwadago a yanar gizo [wato freelance work] hanya ce wacce ake samun kudi kwarai da gaske. Domin masu rubutu suna yin kwadagonsa, haka ma masu hada shafukan yanar gizo, graphic designers, 3D aminators, haka ma masu editing na bidiyo, editing na hotuna, hada applications na waya da sauransu.

Kai duk wani irin aiki da ka sani wanda ake yi da nau’ra [wato skills] to za a iya yin kwadagonsa ta yanar gizo.

Kana gida Kano, za ka yi wa wanda ke Amurka ko Burtaniya kwadago kuma ya biya ka.

Shi yasa za ku ga yanzu haka mutane sun dage wurin koyon digital skills domin su rinka samun ‘yan kudade ko da kuwa suna karatu ne a makaranta.  

3. Rubutu a yanar shafin gizo

Rubutu a shafukan yanar gizo shi muke cewa Blogging, kuma babbar hanya ce ta samun kudi a yanar gizo. Amma fa ba a samun kudi da ita dare daya kamar sauran hanyoyi.

Dole kana bukatar ka iya wadansu abubuwa masu ‘dan yawa kafin ka fara iya blogging har ya rinka kawo maka kudi.

Kana son ka iya;

  1. Rubutu mai kyau da tsari
  2. San yadda za ka yi posting
  3. Ka dan san wani abu akan SEO
  4. Ka iya rubutu kamar kana magana da makaranci

Bayan ka iya wadannan, kana kuma da bukatar ka samu wanda zai bude maka shafin naka ya saita maka shi. Sai ka nemi darasi [topic ko niche] guda daya ka mayar da hankalinka a kansa.

Ka rinka rubutu kullum-kullum a kansa, kana yin sharing na wadannan posts din naka a social media.

Ya kasance kuma niche din naka ba local ba ne, son samu da turanci, spanish, german, french, portugues, ko wani yaren ka ke son rubutun wanda hakan zai taimaka maka wurin samun makaranta wadanda za su rinka kawo maka kudade daga kasashen waje.

4. Gina shafukan yanar gizo da applications

Gina shafukan yanar gizo [web design and development] da kuma hada applications na waya [app development] hanyoyi ne wadanda ke kawo wa masu  yinsu kudi mai gwabin gaske.

Sai dai in da damuwar ta ke, dole sai mutum ya fara iya kwamfiyuta sannan ya je ya koyi programming, daga nan sai ya zabi inda zai karkata wato hada shafuka ko apps, ko kuma softwares.

Kafin mutum ya kai ga samun kudi da wadannan zai dau lokaci kwarai da gaske, amma ko tantama babu, duk ranar da ya fara samun kudi, to fa shi wannan kawai ya haye.

Domin abubuwan nan suna kawo kudi kwarai da gaske musamman ma masu hada applications da softwares.

In dai kana da sha’awa akan programming, to son samu ka gwada zabar sashe guda ka mai da hankali a kansa.

5. Bude tashar YouTube kana dora bidiyo

 Kowa ya san cewa ana samun kudi da tashoshin YouTube, amma ba kowa ne ya san yadda zai bude tashin tashar ba, da kayan daukar bidiyo da editing da zai nema, da wadanda za su taya shi gudanar da tashar da ma hakurin da zai yi ya cigaba da aiki baya samun ko anini har tasharsa ta bunkasa.

Mafi yawan lokuta ana fada wa mutane dadin da ke tattare da samun kudi ne a YouTube ba tare da yi musu bayani akan irin rukukin da ake ketawa ba kafin a kai ga wannan matakin.

To, ko tantama babu in dai za ka bude tasha a YouTube ka rinka hada bidiyo kana dorawa, kana share a social media, kana yin YouTube SEO, to tasharka za ta bunkasa watarana ka samu kudi da ita.

Sai dai kafin ka kai ga samun kudin da ita, za ka yarfe kwarai, amma kuma bayan wuya sai dadi.

6. Saye da Sayarwa [Trading]

Trading dai na nufin saye-da-sayarwa, amma ya karkasu nau’i-nau’i, wasu na trading na kudade [wato masu sayen kudaden waje, in darajarsu ta hau sai su sayar]. Yayin da wasu kuma saye da sayar da hannun jari [stock] suke yi. 

Wasu kuma kudin cryptocurrency suke trading. Amma mafi akasari mutane sun fi yin Forex trading.

Ko-da-ya-ke akwai babbar kasada game da trading, amma dai ana samun riba mai gwabi in aka dace.

Kuma shi ka’idar trading ita ce; ba ka saka kudin da ba naka ba ko kuma kudin da ba za ka iya jurar narkewarsa ba.

Kammalawa

A nan zan daka ba wai don na so ba, kuma dama na fada muku zan kawo muku fitattun hanyoyin samun kudi a yanar gizo kamar guda 6 ko 7 na yi muku bayani a kansu.

Bayan na yi bayanin, sai mu kammala rubutun nan namu.

Sai dai zan so yi muku da bushara cewa: wadannan hanyoyi fa ba iya su kenan ba, akwai karin wasu gomansu. Da za ku matsa da bincike da kun binciko su.

Allah ya kara wa Annabi daraja.

Post a Comment

Previous Post Next Post