Kanunfari da Amfaninsa da Fa'idar Tsarki da Matsi da Kanunfari

Kanunfari
Kanunfari

‘Yan itatuwa [ko ma itatuwan] ba kowanne ne daga cikinsu ake sarrafashi da amfani da shi ta sigogi masu tarin yawa kamar kanunfari ba.

Bisa wannan dalilin, yau mu ka ware shafi guda domin mu yi tattaunawa ta musamman akan kanunfari, kai har ma da bayar da hadin magungunan da ake hadawa da shi.

{toc} $title={Abubuwan Da Ke Ciki}

Menene Kanunfari

“Kanunfari dai sinadari [‘dan itace] ne da ake amfani da shi a abinci don ya kansasa shi, ana daka yaji da shi don ya kansasa shi, ana saka wa a shayi don ya kansasa shi, sannan ana mahadi [ko] maganin sanyi da shi hadi da saka shi a sauran abinci.”

Amfanin Kanunfari

Likitoci sun tabbatar da cewa kanunfari na da matukar amfani ga ‘Dan Adam. Bugu-da-kari, yana motsa sha’awa, yana kara wa maza lafiyar mazakuta da karfinta, yana inganta lafiyar maniyyin namiji hadi da inganta kwararar jini zuwa ga mazakutar namiji.

Ba fa a iya nan amfanin kanunfari ya kare ko ya tsaya a jikin ‘Dan Adam ba, a’a, akwai karin alfanunsa.

Kanunfari kunshe ya ke da sindarin da ke yaki da cututtuka da bunkasa garkuwar jiki. Shan ruwansa na taimakawa wurin narkar da abinci cikin sauri da dakile cutar olsa.

Ga maza da mata wadanda ke fama da matsalar kiba da teba, to, shan ruwan kanunfari na bada muhimmiyar gudunmawa wurin rage kiba da teba ga mata da maza.

Also Read: Alamomin Shigar Ciki na Sati Daya, Sati Uku, da Watan Farko

Shan ruwan kanunfari na yin maganin cutar kwalara, da jiri, da saisaita sukari ciki jini, da tabbatar da lafiyar hanta.

Kanunfari na kara lafiyar kashi, da dakile kamuwa da cutar sankarau ko ciwon kansa.

Hakika amfanin Kanunfari a jikin ‘Dan Adam yana da matukar yawan da in lissafi za a yi, to, sai a yi littafi guda a kansa. Mu dai za mu tsaya a nan domin shiga wani babin.

Amfanin Kanunfari ga Mata (da budurwa)

Kanunfari na da matukar amfani ga mata. Shi yasa zai kyautu mace ta rinka shansa [ko da jifa-jifa ne] domin irin alfanun da ya ke da shi.

Daga cikin amfanin kanunfari ga mata akwai karin ni’ima; duk macen da ta juri shan kanunfari [kada ta sha sama da itace hudu kullum] to lallai za ta yi ni’ima kuma megida zai ji dadin mu’amalar jima’i da ita.

Ga macen da kuma ta ke fama da matsalar rashin kwakkwaran kwan haihuwa [wanda shi ke jawo rashin daukar ciki] to ta juri shan kanunfari kullum [kada ta sha sama da itace hudu] da yardar Allah sai a ga ta samu rabo.

Bugu-da-kari knunfari na rage saurin tsufa. Kai yana ma taimakawa wurin rage kiba da karin kuzarin mata yayin jima’i.

Ga macen da ta ke fama da ciwon mara yayin jinin al’ada kuma kwanakin da ta ke shafewa tana al’ada su ke tsayi, to, ta juri shan kanunfari domin yana rage tsayin kwanaki da ciwon mara yayin al’ada.

Har ila yau kada ku yi zaton shi amfanin kanunfari iya ga mata ya tsaya, a’a, har maza ma yana yi musu amfani. Yanzu za mu tsallaka zuwa babi na gaba.

***

Za mu takaita jawaban wannan wallafa ta mu zuwa kalmomi dubu daya. Amma kafin haka ka wasu sirrika [hade-hade] wadanda ake hadawa da Kanunfari.

Dabino da Kanunfari

Shin ko kin san cewa yin hadin kanunfari da dabino na kara wa mace ni'ima ta kololuwa kuwa?

To ga hadin, “Ki samu kanunfarinki da dabinonki sai ki sa a mazubi ki jika su. Bayan sun tsumu sai ki na diban ruwansu kina sa zuma a ciki kina sha.”

Hakan zai kara miki ni'ima kwarai da gaske. Za ki gode wa mawallafin nan ki godewa Allah in dai ki ka jarraba hadin nan.

Matsi da Kanunfari

Shin ko kin san cewa kanunfari ba iya matsin gaba ake yi da shi ba? 

To, in ba ki sani ba ana amfani da shi wurin ciko gaba.

Ta yaya ake yi? Ga bayanin nan kasa.

Don matsi da kanunfari sai ki samu kanunfari ki kakkarya ko daka shi sama-sama, sai ki samu garwashi ki kai daki, ki debo kanunfarin nan 

ki zuba akan garwashin. Daga nan sai ki tsugunna a kan hayakin.

Kamar yadda aka shaida mana, yana maganin warin gaba da matsin gaba.

Kuma shan kanunfari [in an jika shi] yana sa gaban mace ya ciko, sannan yana maganin sanyi.

Amfanin Tsarki da Kanunfari

Ana yawan samun mutane wadanda ke yin tambaya game da tsarki da kanunfari, shin ko menene amfaninsa?

Tabbas in dai tambayarki kenan, to, yau na zo miki da cikakkiyar amsa.

Ruwan kanunfari ana yin tsarki da shi ne domin magance infection na mata. Da fari dai za ki samu kanunfarinki da ganyen magarya sai ku zuba su a mazubi, ki kawo ruwa ki zuba musu, sai ki barsu su yi kamar [ko fiye da] sa'a daya.

Bayan lokacin ya cika, sai ki debi ruwan ki rinka tsarki tsarki da shi, in son samu ne ki yini kina yi.

Kuma ba sau daya za ki yi ki dena ba, ki cigaba har sai kin tabbatar kin rabu da infection din.

Wannan shi ne amfanin tsarki da kanunfari. Da fatan kun amfana da wallafawar nan tamu.

Kammalawa

A nan zan dasa aya a cikin wannan wallafa ta mu ta yau, kada ku manta a cikinta mun yi muku cikakken bayani akan kanunfari, da amfaninsa ga maza da mata har ma da ‘yammata.

Sannan mun kawo muku hade-hade da ake yi da shi Kanunfarin.

A karshe muna addu’ar Allah ya kara wa Annabi Daraja. Ku hadu ku ce ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post