Ciwon Sanyi da Alamominsa Sai Maganin Infection Kowanne Iri

Maqanin Ciwon Sanyi
Ciwon Sanyi


Duk wata cuta da ku ka sani, Allah shi ne wanda ke saukar da ita. Haka kuma babu wata cuta da ya saukar a doron kasa ba tare da maganinta ba.

Kalmar 'Sanyi' ba wata kalma ce bare ba ga Hausawan duk duniya. Kuma dauke take da ma'anoni har guda biyu, a Hausar wata baryar ma sai a samu ma'anar ta zarta biyu.

Ina [ko muna] da kwanan sanin cewa titunan unguwanninmu, garuruwanmu, da kauyukanmu cike suke da taratsin amsa kuwwar masu tallan magunguna iri-iri –musamman na gargajiya. 

Daidaikun cikinsu na da lasisi da ke nuni da cewa hukumar NAFDAC ta tantance maganinsu, ta sahale su sayar da shi duk da ba ta basu irin dose din da ya kamata a rinka sha ba.

{toc} $title={Abubuwan Da Ke Ciki}

Yayin da mafi akasari ba wata sahalewa da suke da ita, illa iyaka neman na abinci da suke yi kurum. A matsayinka na mai sayen magani irin wannan za ka siya ne bisa kila-wa-kala, wato in ka yi dace ka samu sauki, in an samu matsala ka sha wuya. 

Domin kamar yadda wani likita ya bayyana su magungunan gargajiya ba su da wata iyaka, illa dai mutane suna shansu fiye da bukatarsu (overdose) wanda hakan na da illa ga lafiya.

Sannan, mafi akasarinsu na haifar da matsalar dattin koda ko kuma ta lalace.

******

Ina yi mana maraba da zuwa shafin nan namu mai albarka, wanda a cikinsa yau za mu yi cikakkiyar tattaunawa akan lalurar sanyi, alamomi, magungunan sanyi na bature, na gargajiya, da sauransu.

Ba tare da wani dogon surutu ba, za mu fara ne da yin bayani akan menene sanyi.

Menene Sanyi

In ba ku manta ba, a baya na karkasa sanyi zuwa gida biyu. Amma a zahirin gaskiya ya wuce biyu sai dai kawai mu takaita saboda ko makaranta za su gajiya.

In aka ce sanyi ana nufin: “Sauyin yanayi na dari da ke wanzuwa a Yammacin Afirka sakamakon iska da hazo da ke busowa daga gabar teku, kuma yana farawa daga Disambar kashen shekara zuwa Fabrairun sabuwar kowacce shekara.”

Recommended Reading: Ciwon basir, alamominsa, da maganin ciwon iri-iri don kawar da shi 

Shi irin wannan sanyin yana haifar da bushewar fata, bushewar makogwaro, mura da tari, da tsatstsagewar fata ga maza da mata, yara da manya.

Menene Sanyin Mara

A daya barin kuma sanyin mara na nufin ciwon sanyin da maza ke dauka sakamakon tarawa da mace - ko kuma tsohon mataccen maniyyi ya dankare musu a mararsu.

A wata ma’anar kuma, “Ciwon sanyi na maza shi kuma mafi akasarin lokuta ya kan sa namiji kurajen kan azzakari, kankancewar gaba, daukewar sha’awa, fitar farin ruwa daga kwarkwaron azzakari da sauransu.” – SeeyBlog.

A bangaren mata ma suna iya kamuwa da sanyin mara sakamakon tarawa da ake da su, da kuma taruwar mataccen maniyyi a mararsu.

Maganin Sanyi

Shi dai hadin maganin sanyin nan da za na kawo muku ingantacce ne sai wahalar hadawa ga wanda ya gaza samun mahadan.

Ku nemi:

 1. Jar kanwa
 2. Ganyen dogon yaro (bishiyar turare)
 3. Ganyen goruba
 4. Da ganyen ciyawar baru'ku

Yadda Ake Hada Shi

Abu na farko da za ku yi shi ne ku dora tukunya a wuta sannan ku kawo ruwa mai kyau ku zuba a ciki.

Sai ku kawo ganyen goruba, dogon yaro, da ganyen ciyawar baru'ku din nan ku zuba a ciki.

Kana, ku debo jar kanwarku madaidaiciya ku zuba a ciki sai ku tafasa har sai ya tafasu.

In an tabbatar ya tafasu, to sai a sauke a barshi ya yi sanyi tukunna.

Sai a na diban ruwan ana sha kullum sau biyu [safe da dare] har na sati daya ko biyu.

Da yardar Allah za a samu waraka daga lalurar sanyin da ta bi ta addabi mutum.

Menene Sanyin Mata (Infection)

Tabbas Ubangiji na matukar kaunarmu bisa sanya tsabta da ya yi a matsayin cikon addini.

Wasu matan na kallon tsabtace bandaki a matsayin aikin wahala, amma wallahi ba aikin wahala ba ne.

In ka shiga kauyuka da karkara, sai ka taras lalacewar lamarin ta yi kamarin da sai dai mu ce Allah shi sawaka.

Mata na kamuwa da ciwon sanyi infection ne sakamakon amfani da suke yi da kazamin bandaki, suna fitsari a wuri maras tsabta mai dauke da kwayoyin cuta.

“Sanyi infection na mata ciwo ne da ke sanya mace ta rinka kurajen gaba, ta na jin gabanta na kaikayi, ko gabanta ya na fidda farin ruwa mai wari, ko kuma ta na fama da matsalar rashin sha’awa ko rashin gamsuwa yayin da ake saduwa da ita da sauransu.” - SeeyBlog

Bisa wannan dalili ya zama wajibi duk wata mace wacce sanyi (infection) ya kama ta ta nemi magani domin samun waraka.

In kuma kai maigidanta ne, sai ka fahimci tana fama da sanyin nan, ka karbo mata magani ta gwada sai ka ga an dace.

Alamomin Sanyin Mata (Infection)

A turance dai ana kiran alamomin kowacce irin cuta da ‘symptoms’, to shi ma ciwon sanyin mata wato infection na da irin nasa alamomin wadanda in ba ku sani ba ga su nan kasa.

Daga ciki akwai:

 • Ciwon mara mai tsanani
 • Daukewar sha’awa
 • Fitar jinin al’ada da wari baki-kirin
 • Kurajen gaba
 • Fitar wani ruwa mai wari daga gaban mace
 • Jin zafi yayin da ake tarawa da mace
 • Sannan yana hana haihuwa in ya yi karfi

Mun zabi takaita yawan alamomin sanyi infection domin wadannan da muka jero su ne fitattu wadanda kusa kowa ya sansu.

Abin Da Ke Kawo Sanyin Mata (Infection)

Shi lalatar sanyin mata ita ce; namiji zai iya kwasar sanyin daga wurin matarsa. Yayin da shi kansa namijin in yana fama da ciwon sanyin zai iya shafa wa matarsa.

Amma akwai wadansu abubuwa da ke kawo ciwon sanyi (infection) na mata, daga ciki akwai:

 1. Yin fitsari a bandaki marar tsabta
 2. Yin tsarki da ruwan zafi ko sanyi ya yi yawa
 3. Jima’i da mai cutar (mace ko namiji)
 4. Sai cin danyar albasa.

Ba fa iya su kenan ba, da za ku tambayi likita da ya kara ba ku misalan abubuwan da ke kawo ciwon sanyi na mata.

******

Madallah.

Mai karatu ina fatan kana bibiye da mu a cikin wannan cikakken jawabi namu akan lalurar sanyin mata infection.

Also Read: Alamomin shigar ciki na sati daya, sati uku, da watan farko

Abin da kuma zai biyo baya shi ne magunguna iri-iri na Hausa wadanda ke magance lalurar sanyin mata infection.

Ku yi sani cewa: Mun yi nasarar zakulo hade-haden magungunan nan ne bayan yin dogon binciken kwakwaf. Duk da ba mu da cikakken garanti akan aikinsu amma dai wadanda su ka bayar da su sun bada garanti.

Maganin Sanyi Infection

Nau'in hadin maganin nan yana yin maganin sanyi na mata (infection) kwarai da gaske, kawai ku jarraba.

Domin hada shi sai ku samu:

 • Sassaken sanya
 • Da garafuni

Yadda Ake Hada Shi

Abu na farko da za ku fara yi sai ku zuba su a cikin tukunya, ku tafasa har sai sun tafasa tukunna.

Sai a sauke, a bari ya huce.

Bayan ya huce sai ku na diban ruwan maganin kuna sha kullum sau biyu a rana, amma fa rabin kofi daya ake sha.

Maganin Sanyi Infection II

Shi ma dai wannan hadin an tabbatar da cewa yana magance ciwon sanyi na mata amma fa da yardar Allah.

Ku samu wadannan abubuwan:

 1. Ganyen gwanda
 2. Tsamiya
 3. Citta
 4. Tafarnuwa
 5. Gishiri

Yadda Ake Hada Shi

Kafin ku yi komai ku fara samun ruwan dumi, sai ku kawo gishirin nan ku zuba a ciki, sannan sai ku dauko ganyen gwandarku ku sa shi a ruwan dumin nan ku wanke - amma kada ku dirje shi.

Dalilin da yasa ake bukatar ku wanke shi saboda ku fitar da datti da sauran cututukan da ke jikin ganyen.

Abu na gaba sai ku samu ruwa [kamar lita goma] ku zuba a cikin tukunya sannan ku kawo ganyen gwandar nan, citta, tafarnuwa, da tsamiyar nan ku zuba a cikin ruwan.

Daga nan sai a kawo gishiri a zuba cokali biyu [babban cokali], sai a tafasa har sai ya tafasu kwarai.

Sai a sauke rinka diban ruwan ana sha kullum sau biyu [safe da daddare].

A kula: Kada a saki jiki wurin shan ruwan maganin har sai an koshi, a rinka samun kamar rabin kofi ko karamin kofi ana sha.

Maganin Sanyi Infection III

Wannan hadin maganin shi ne mafi sauki a cikin duk wasu hade-haden magungunan sanyi da muka kawo.

Sannan kamar yadda aka bayyana, an tabbatar da yana aiki sosai amma fa da yardar Allah.

Ku samu:

 • Ganyen zogale
 • Madara, nono, ko zuma

Yadda Ake Hada Shi

A nemi danyen ganyen zogale sai a dafa shi, in ya dahu sai ku mashe shi ku tace ruwan zogalen ku aje gefe.

Sai ku kawo maradarku, ko nono, ko zuma ku zuba a cikin ruwan zogalen ku shanye.

Amma fa ku debi ruwan yadda za ku iya shanyewa.

Ku cigaba da yin hadin nan kullum har tsawon sati daya zuwa biyu, da yardar Allah za a samu waraka.

Maganin Sanyi Kowane Iri

Wata baiwar Allah ta wallafa wani nau'in maganin sanyi wanda ta bayar da tabbas kan cewa yana yin aiki.

Shi dai wannan hadin maganin sanyi ne kowanne iri musamman sanyin da ke haifar da mura, tari, ciwon gabobi, kaikayin jiki da rikewar baya da kwankwaso.

Sa'annan yana da saukin hada wa kwarai da gaske.

Domin hada shi sai ku nemi:

 • Tafarnuwa -amma garin ta
 • Nono kindirmo ko madara ta ruwa

Yadda Ake Hada Shi

Ku samu garin tafarnuwa sannan ku hada da nono rabin kofi, sai ku debi garin tafarnuwar nan cokali biyu ku zuba a cikin nonon ku juya.

Daga nan sai a sha.

Ku yi irin wannan hadin sau biyu a rana har na tsawon akalla kwana bakwai da yardar Allah za a samu sauki.

Sai dai: Muna sane da cewa ba kowa ne ke son sha ko cin tafarnuwa ba, kai wasu ma ko warinta ba sa so.

Ga wadannan sai ku gwada sauran hade-haden magungunan sanyi na gargajiya da za mu kawo a kasa.

Maganin Sanyi Kowane Iri II

Shi ma dai wannan hadin maganin gargajiyar an ce yana magance sanyi kowanne iri ne ga maza da mata.

Sannan, wanda ya wallafa shi, ya ce mutum zai iya hada shi ya gwada ko da kuwa ba shi da lalurar sanyi.

Amma dai, duk gaggawar asara ai ta jirayi samu ko!

Domin hada shi, sai ku nemi:

 • Man tafarnuwa
 • Danyar citta
 • Zuma
 • Khaltuffa

Yada Ake Hada Shi

Abu na farko da za ku fara yi shi ne ku samu tasa ku zuba ruwa kofi biyu a ciki, sai ku dora a wuta.

Daga nan sai ku samo cittarku manya guda biyu danya ku dake ta.

Ku debo dakakkiyar cittar ku zuba a cikin ruwan nan da ke kan wuta, ku bar ta ta tafasa sannan ku sauke.

Sai ku na tsiyayar ruwan cittar nan a kofi, kuna saka zuma cokali 8, da man tafarnuwa cokali 4, da khaltuffa shi ma cokali 5 kuna juyawa kuna sha.

Ku rinka yin hadin safe da yamma kuna sha har na wasu 'yan kwanaki kamar biyar ko 'dai yadda ya sauwaka.

Da yardar Allah za ku samu sauki.

Maganin Sanyi Kowanne Iri III (Na Asibiti)


A likitance akwai magunguna iri-iri da likitoci ke bai wa marasa lafiya su samu sauki daga lalurar sanyin da take damunsu.

Akwai wani magani mai suna Ofloxacin wanda ake amfani da shi wurin magance ciwon sanyi kowanne iri ne.

An ce irin cututtukan da ya ke warkarwa na sanyi sun hadar da:
 1. Cututtukan fata
 2. Mahaifa
 3. Mafitsara
 4. Kashi da sauransu.
Sai dai: Ko da wasa kada ku je ku sayi maganin nan har ku yi amfani da shi ba tare da kun tuntubi shawarar likita ba. 

Sannan, ana iya samunsa akan kudi 1,500 ko 2,500 har zuwa sama sakamakon karin tsara kaya da aka samu.

Ku kuma karanta kwalin maganin domin fara fahimtarsa.

Kammalawa

Alhamdulillah. A nan na ke sa ran dakatawa da jawabin nan dangane da lalurar sanyi da magungunanta na gargajiya har ma da na asibiti.

Nan gaba kadan, ina sa ran za mu zauna da wani likita har ma da wasu masu magungunan gargajiya domin kawo muku karin wasu magungunan na sanyi.

Amma kafin haka, zan shawarceku da ku fara tuntubar likita kowanne lokaci kafin ku yi amfani da kowanne irin magani.

Allah ya kara wa Annabi daraja.

Post a Comment

Previous Post Next Post