Kana Son Iyawa? To ka ji Yadda Ake Chatting da Mace Cikin Sauki

Yadda Ake Chatting da MAce

{toc}

Yau ma dai ga mu Allah ya kara hada mu a cikin wani sabon darasin wanda za mu yi wa matambaya karin haske akan chatting da mace.

***

Wai fa sai ka samu har zuwa yau akwai wadanda ke da matukar bukatar karin haske akan chat da mace musamman a kafafen sada zumunta irin su Facebook, WhatsApp, Twitter, Telegram, da sauransu.

Yayin da wasu kuma baki daya ma ba su da kwarin gwuiwar da za su iya tarar mace su zayyana mata abin da ke tafe da su "irin matsoratan cikin nan namu".

Ba zai kasance abin mamaki ba in har aka samu irin wadannan mutane a cikinmu domin Allahn da ya haliccemu [mutane] ya haliccemu ne da yawa kwaraida gaske.

Sai dai kamar yadda wasu su ka dauka [ko in ce bakin lamarin], chat da mace ba shi da wata wahala, kuma yadda ake yinsa ma ba wuya gareshi ba.

Amma zan so sanar da kai wasu abubuwa masu matukar muhimmanci wadanda ya kamata ka fahimcesu kafin ka fara mu'amala da mata a kafafen sada zumunta musamman bangaren soyayya.

Kafin Fara Chat da Mace

  1. Ya kasance kana da aji
  2.  Za ka iya bambance mace da gardi mai akawun din mata
  3.  Kuma ba ka yawan fito da kwadayinka fili har abin ya wuce na Muhammadiyya
  4. Za ka iya jaraba macen da ku ke mu'amala da ita ka gane namiji ne ko mace
  5. Ba kuma za ka bude bakin aljihunka ba kamar sabon wawa saboda ka hadu da wata zallaziyya a kafafen sada zumunta.


Wadannan abubuwan guda biyar suna da matukar muhimmanci kwarai da gaske.

Abu na farko: dai ya zama wajibi a gareka ka kasance kana da aji kamar yadda mata ke da na su. Kuma ka iya jan ajinka kai ma.

In ka aike wa da mace sako, ka ga ta dau lokaci ba amsa, to in ta dawo maka da shi kai ma sai ka sha masa kamshi sai ka 'dau lokaci kafin ka mayar da martani.

Sa'annan yayin da ka ke magana da ita, kada ka rinka saurin rubuta duk abin da ya fado maka a rai, ka fara tacewa tukunna.

Ka kuma rinka yi mata magana fahimtacciya ba magana mai cike da jahilci da tumasanci ba domin mai aji bai zancen kara zube musamman a social media.

Abu na biyu: shi ne mutum ya kasance ya fahimci wani abu game da maza masu amfani da hotunan mata da sunansu suna damfarar mutane a kafafen sada zumunta.

Su irin wadannan mazan suna yawan bude asusu suna aikawa maza sakon abota, da ka karba sai su fara jan ka da hira, har sai ka saki jiki da su sannan sai su ce maka ka tura musu kudi ta kati ko akawun.

To, kada ka yarda ka yi haka. Dalilin da yasa ba sa bayar da lambar waya saboda za a kira a ji maza ne, sai su yi ta ja maka rai akan cewa sai ka tura musu kati sannan ka tura musu lambarka sai su kira ka.

Da zarar ka tura sai su yi block dinka. Shi ke nan sun wanki gara. Don haka ya kamata ka fahimci da wa ka ke chat ko za ka fara chat din tukunna.

Abu na uku: shi ne rashin nuna rashin daraja a fili, rashin darajar kuma shi ne fito da kwadayi a fili karara kamar sabon maye. Hakika mu maza Allah ya yi mu da son mata [amma kada ka rinka fito da taka maitar fili kullum] kuma ko limamin unguwarku ne ya ce maka ka fiya son mata, wallahi kawai rainaka kawai ya yi.

Yayin da ka ke hira ta yanar gizo da mace, bai kyautuwa ka rinka bidar hotunan sassan jikinta, bidiyonta na sutura ko yi mata zancen batsa domin tana jin inda ka dosa to ta san a matsayin da za ta aje ka [wato dai kai dan iska ne].

Daga haka tadin ba lallai ya yi nisa ba. Shi yasa duk jarabarka kada ka rinka yawan fito da maitarka fili yayin chat da mace.

Amma akwai lokutan da ba laifi ba ne fito da maitar, domin nisan kwana sai da gwaji!

Abu na hudu: kuma shi ne, ya kasance ka bidi lambar mace musamman wacce ku ke chat da ita a Facebook, in kuma ta WhatsApp ne ka zambada mata bidiyo call domin ka bambance macece ko namiji.

In a Facebook ne, daga lokacin da akawun mai amfani da sunan mata ya ki turo maka lambar waya, to, ka yi amanna da gardi ka ke chat kawai.

Yana da kyau ka rinka tankade da rairaya yayin da ka ke mu'amala da mata a kafafen sada zumunta domin kada ka zurma kamar yadda kwanaki aka yi ta kace-nace saboda gano wani gardi mai amfani da sunan mata a Facebook da aka yi.

Abu na biyar [na karshe]: shi ne kada ka zama wawan sarki ko sabon mahaukaci tuburan saboda ka ga asusun shafin sada zumunta mai dauke da hoton wata zallaziyyar mace ya turo maka da bukatar kudi kai kuma ba wani tunani ka tura.

Mafi akasarin hotunan nan filta ce, kuma an fi samo su a shafin Instagram sai a kawo su Facebook ko WhatsApp a rinka wankar garori da su.

Bida wannan dalili na ke baka shawara da kada ka yi wasa ka zame wa wani ko wata ATM alhali ba ku taba haduwa fuska-da-fuska muraran ba.

Fara Chat Da Mace

Shi fa fara zance [chat] da mace a yanar gizo ba wata wahala gareshi ba muddin ya amince da a yi zance ta hanyar dawo maka da amsar sakonka na farko ko da kuwa bayan sati biyu ne.

Amma zai fi kyautuwa ka fara da yi mata Sallama sai ka aike da sako mai dauke da sallamar a sama kamar haka;

"Assalamu Alaiki Baiwar Allah

"Amincin Allah ya tabbata a gareki. Na samu lambarki a wurin abokina [ko a cikin group] shi ne na yi tunanin yi miki magana domin mu gaisa mu san juna.

"Ni dai sunana Muhd Kabir mazaunin jihar Kano. Da fatan ban takura miki ba baiwar Allah."

Daga haka sai ka tura mata, ina da yakinin za ta dawo maka da amsa domin ka yi mata magana ne cikin mutunci da mutuntawa, ka kuma nuna mata ba fa da neman soyayyarta ka zo ba. Kawai so ka ke yi ku san juna.

Bayan ta dawo maka da amsa sai ku cigaba da hira, kuna 'dan tadi. Kada ka uzzura mata da yawan messages, guda biyu kullum sun isa har ta saki jiki da kai.

To, daga baya za ka iya cewa kai fa wallahi ta yi maka, amma kafin ka fadi haka dole sai ka fara da yaba kyawunta kullum musamman in ka lallabata ta turo maka hotonta.
Wani Sirri

Su fa mata da ku ke gani Allah ya yi su da son a yabe su, a kambama su domin suna son hakan. Duk munin mace in dai za ka yaba ta to wani fasa mata kai ka ke yi.

Saboda haka zai fi kyau in dai so ka ke yi ku yi soyayya da mace a kafar sada zumunta to ka fara da yabonta lokaci zuwa lokaci, kuma ku fara 'dan daukar lokaci a tare a kafar kafin ka fito da abin da ke cikin ranka.

Kammalawa

Shi fa chat da mace bashi da wata wahala. Kuma kada ka sa wa kanka takunkumi akan cewa lallai sai abin da mu ka tattauna a cikin rubutun nan shi za ka yi.

No, kawai ka zabi hanyar da ka ke gani ita ce mafi daidai da daidaito a gareka ka yi amfani da ita in dai za ta kai ka ga inda ka ke son zuwa.

Da wannan zan rufe rubutun nan. Da fatan Allah ya yafe mana kurakuranmu ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post