Yadda Ake Gane Anci Budurwa

Yadda Ake Gane Anci Budurwa

Lallai zamani ya ɓaci, al'ummarmu ta matukar lalace. 

Yau, wasu basu ɗauki zina a bakin komai ba, a otal-otal kullum sai an sukwane ƴammata da dama waɗanda ko auren fari ba su gani ba.

{toc}

Kuma hakan ba ƙaramin koma baya ba ne ga al'ummarmu, duk ko wanda ya ce ƙarya ne to munafuki ne shi wallahi.

Ba mamaki kai ka lalace, ka ɓaci, amma fa ka yi sani cewa akwai dubunnan ƴaƴa mata waɗanda ba su lalace ba.

Ina shawartakarka da kada ka yi sake ka zama silar lalacewar ƴaƴan mutane.

Domin da wuya abinda ka shuka watarana ba ka girbe shi ba, kai, ko ba ka girbe ba, ƴaƴanka sai sun girbe maka.

Mu shuka alkhairi!

***

Yau, a cikin wannan darasi wata tambaya ce mai wuyar bayar da amsa na ke son amsa muku ita kai tsaye.

Ba a son raina zan baka amsar tambayar nan ba, amma tun da ka matsa, ai shi kenan, mu je zuwa...

Zan so ku yi mini addu'ar neman sa'a.

***

Wacece Budurwa

Ba zan fara ba ku cikakkiyar amsar da kuke biɗa ba, ba tare da na sanar ku wacece budurwa ba.

“Budurwa ita ce mace yarinya wacce bata taɓa sanin namiji ba. Wato namiji bai taba tarawa da ita ba.”

Kuma budurci babu ruwansa da shekaru, wata na iya riƙe nata budurcin har tsawon shekaru wajen 30 ba tare da ta san namiji ba, sai dai ta ji labari.

Abin zai matuƙar baka mamaki in ka ji irin tsawon lokacin da wata ta shafe ɗauke da budurcinta a rayuwa ba tare da sani  ɗa namiji ba har sai da ta yi aure.

Wata kuwa tun kafin ta kai shekaru 15 take rasa budurcinta.

Ina na ce muku budurci, ba fa ina nufin fatar budurci ba.

A'a

Ina nufin sanin ɗa namiji a jima'ince!

Yadda Za Ka Gane Wani Yaci Budurwarka

Zan so ku gafarceni sakamakon yin amfani da waɗansu kalmomi wadanda da ƙa'idar al'adar Hausa da Musulunci sun saba wa ƙa'ida domin kalmomi ne na batsa.

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wurin sanin shin mace ta san namiji ko ba ta sanshi ba.

Daga cikinsu akwai:

# Mu'amalarka

Tun daga kan mu'amalarka da mace za ka fahimci waɗansu abubuwa masu tarin yawa a tattare da ita.

Za mu iya cewa mata sun waye a zamanin nan ƙwarai da gaske. Amma wayewar mafi akasarin lokaci koma baya ce.

Yayin da kake mu'amalantar macen da za ka aura, yana da kyau ka yi mata waɗansu gwaje-gwaje domin tabbatar da cewa ba mazinaciya za ka aura ba.

Ka yi sani cewa, wasu na iya tsallake duk wani irin gwajin bazata da za ka yi musu kuma suna aikata masha'ar.

Wannan ya sa ko da ka yi mata duk wasu tests a mu'amalance, sai ka ƙara da neman zaɓin Allah domin ya zaɓa maka mafi alkhairi.

Za ka iya yi mata tayin ta baka haɗin kai domin ku yi zina ko da sau ɗaya ne, ka nuna mata aurenta za ka yi da gaske.

Kai in da hali ma ka gayyace ta wani otal, ka kama ɗaki, ka jira ta.

In dai ta yarda ta je, to da akwai matsala, domin ko an yi auren ba lallai ku samu nutsuwa da juna ba.

Za ka iya gwada ta ta hanyar nuna mata eh ba wata matsala don kun sha minti ka yi wasa da jikinta.

In har ta amince, to, ko dai tana matukar ƙaunarka ko kuma da akwai matsala.

Recommended Reading: Labarin Cin Duwawun Hajiya

Abin Lura: abin da yasa mafi akasarin ƴammata ba sa iya cewa a'a yayin da saurayin da suke matuƙar so ya yi musu tayin masha'a, saboda kada su ɓata masa rai ne. In ka fahimci wannan ne dalilin baka kanta, sai ka yi mata nasiha, ku cigaba da mu'amalarka.

Haƙiƙa duk yadda ka kai da gwajinka, muddin ba ka nemi zaɓin Allah ba to sai yadda hali ya yi.

Gare ku Maza: kada ka yi tunanin za ka kasance mazinaci, kuma Allah ya baka wacce ba ta zina, shi fa Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Mai haɗa kowa da daidansa ne.

# Yawan Son Taɓa Jikinka

A nan kam matan birni zan fara taɓawa tukunna, su ne ba su ɗauki taɓa jiki  saurayi wani abu ba.

Wasu samarin ba sa son mace ta rinƙa taɓa su musamman in ta kasance ba muharramarsu ba.

In kana daga cikinsu, kuma ka fahimci halin budurwarka kenan, to, in son samu ne ka ja hankalinta a kan ba ka son ta rinka tattaɓe ka babu dalili.

Domin daga ɗan taɓe-taɓe ake taɓe ko ina. Yana da kyau mu mutunta jikkunanmu kamar yadda shari'a ta faɗa.

# Yi Maka Zancen Batsa

Kamar yadda wani bawan Allah ya taɓa faɗa mana, ya ce: duk macen da ta cika zancen batsa da wuya ta bari wani ya yi amfani da ita.

Saboda mafi akasarinsu baki da su raurau, amma ba su cika yarda a yi iskanci da su ba.

Don haka in dai budurwarka tana a cikin wannan babin na ƴammata masu surutu musamman faɗar batsa, abinda za ka yi mata shi ne: ka rinƙa kan hankalinta ga barin yin zantukan batsar.

# Yawan Kula Maza

In har budurwa ba ta yi aure ta fito ba, yana da kyau ko babu yawa ta rinƙa kare kanta da mutunta kanta, hadi da taƙaita adadin mazan da za ta rinka kulawa.

Ba kowanne ma'ari ne ke son mace mai shegen kule-kulen maza ba, mace marar kamun kai.

Saboda hankalinsa ba zai taɓa kwanciya da ita ba, bayan aure ko ƙaƙa ya ga ta fita tunani zai za ta tsaya kula wasu mazan.

Amma saboda mace tana kule-kulen maza hakan ba shi zai baka damar zarginta da aikata zina ba.

# Turo Hotunan Batsa

Sai tsabar rashin sani ciwon da rasin darajar kai ya zo, sannan maganar tura hotuna da bidiyon batsa za ta shigo.

Wasu matan cikin sauki duke faɗawa tarkon maza, su tura musu hotunan tsiraicinsu ko bidiyo.

Hakan alama ce da ke nuni da cewa ita wannan macen akwai matsala a lamarinta, domin ba ta san ita wacece ba rankatakab.

Zinar zahiri daban, haka ma zinar chat, kuma duk sunansu zina.

Duk budurwar da ka bukaci bidiyo ko hoton tsiraicinta ta kuma turo maka, to, gaskiya da alamu ba macen aure ba ce.

In kuma kai kaɗai ta fara turawa, shi kenan, sai ka ɗiba da haka dama kai ka gani ba wani ba.

Kammalawa

A nan zan dasa aya, ba wai don na so ba. Zan so sanar da mai karatu cewa, ita fa zina yanzu nema take ta zama ruwan dare.

Kuma kai ba ka isa kai tsaye ka gane an yi lalata da budurwarka ba, har sai in da kai aka yi ko kuma ta faɗa maka.

Sai dai in a daren aurenku ta tara da ita ka ji ba budurwa ba ce.

A shawarce: ko me za ka yi, ka nemi yarda da zaɓin Allah su ne kat.

Post a Comment

Previous Post Next Post