Shin Kun San Yadda Ake Gane Mace Mai Dadi? To ga shi Mun Fayyace Muku

Gane Mace Mai Dadi

{toc}

Na ga mazaje da dama sun matukar zakuwa don sanin irin nau’in macen da za ta yi dadi tun kafin su yi aure.

Magana ta gaskiya ni ma namiji ne, don haka ko kadan ban ga laifinsu ba.

Yana da kyau mutun ya san irin macen da zai aura, domin jima’i kansa na daya daga cikin ginshikan aure.

Ban ce ka yi mini musu ba, domin fitaccen marubucin nan Chinua Achebe, cewa ya yi, “In dai gado zai na girgidawa cikin dare to gida zai zauna lafiya.

Ma’ana in dai maigida yana sauke hakkin iyali ta hanyar ragargazarsu kullum cikin dare ta hanyar sauke nauyin tarawa, to, ko tantama babu gida zai yi lafiya.

Amma duk magidancin da ya gaza kashe ‘yan tawayen cikin gidansa cikin dare, to, babu shakka watarana za su caku da uwargida kuma za ta jefar masa da kulli-kullin bakaken maganganu wadanda za su yi matukar sosa ransa.

Shi yasa daga cikin shika-shikan zaman lafiya a rayuwar aure, akwai yin iya kokari wurin sauke nauyin iyali ta fuskar tarawa. 

 * * * 

Mace Mai Dadi

Mata dai kowa ya sani kamar maza, halitta ce ta Allah.

Saboda haka duk wani binciken kwakwaf da za ka yi a kansu ba zai gamsar da kai ba har sai ka san su ta fuskar tarawa tukunna.

Wasu daga cikin maza sun fi yarda da sanin mace ta hanyar yin zinace-zinace (Allah ya tsare mu).

Amma magana ta gasjiya ba za ka taɓa sanin cikakken daɗin mace ba sai ta kasance matarka. Saboda masu iya magana sun ce, "A ci yau, a ci gobe sai matar aure."

Tarawar lokaci ɗaya musamman ta hanyar zina ɗan taƙaitaccen daɗi take samarwa, amma in har aka ce matarka ce, to, sai ma ka gaji da tarawar.

Saboda komai available yake a gareka, ba sai ka sha wahalar komai ba.

***

Nau'ikan Mace Mai Daɗi

Mata sun kasu wajen gida shida, akwai wacce ta fi kowacce wato Harija, akwai mai matsakaiciyar sha'awa, mai ƙarancin sha'awa, mai ruwan ni'ima, da wacce ta fi kowacce daɗi.

Ka ji su:

1). Mai Ƙarfin Sha'awa (Harija)

Duk macen da ka ga mabuyi babban ƴatsan ƙafarta ya fi babban ƴatsan tsayi, to, hakan na nuni da cewa tana ƙarfin sha'awa.

Duk kuwa inda aka samu ƙarfin sha'awa to za a samu ni'ima.

Inda kuwa aka samu ni'ima, to za a samj daɗi.

Ita ce wacce waɗansu ke wa laƙaɓi da Harija, wato sai namiji ke sanar da ita mazantaka a gado.

2). Mai Matsakaiciyar Sha'awa

Duk macen da ka ga mabiyin babban yatsan ƙafarta tsayinsu ya zo ɗaya da babban yatsan ƙafarta, to, hakan na nuni ne cewa ita wannan macen tana da matsakaiciyar sha'awa.

Ba jarababbiya ba ce, amma dai tana da daɗi.

Su irin waɗannan matan sun fi yawa a cikin mata.

Ina son ka yi sani cewa samun nasarar mallakar mace mai matakaicin sha'awa ba ƙaramin abu ba ne. Domin ba kowanne namiji ne hariji ba.

3). Mace Mai Ƙarancin Sha'awa

Duk macen da ka duba mabiyin yatsan ƙafarta ka ga tsayinsa bai kai babban ɗan yasanta ba.

To, haka na maka ishara ne da cewa, ita wannan macen mai ƙarancin sha'awa ce, ba ta kuma da irin masifaffiyar jarabar nan.

Samun irin wannan macen sai maza waɗanda suka dace.

Ba za su taɓa uzzura maka da son tarawa ba, kuma yayin tarawa suna da ni'ima ƙwarai da gaske.

4). Mace Mai Cikakkiyar Dunduniya

Kamar yadda waɗansu masana suka bayyana, sun ce mata masu cikakkiyar dunduniya suna da matukar daɗi da ni'ima.

Ta yadda ake gane irin waɗannan matan shi ne; za ka ga dunduniyarta cike tak dam babu alamar jijiyar agararta a waje.

Hakan ne ke nuni da cewa ita wannan macen kogin daɗi ce, kuma lallai in ka yi nasarar aurenta za ka dade kana jin daɗin rayuwar tarawa.

5). Mace Mai Wushiryar Kafa

"Wushirya ita ce tazarar da ke tsakanin haƙori biyu ko kuma yatsun kafa biyu."

A cikin mata, akwai wata irin mace wacce ake cewa, "Mai Wushirya", ba fa wushiryar baka ce da ita ba.

A'a

Ita wushiryar ƙafa ce da ita.

Ta yadda ake gane ta shi ne; za ku ga akwai tazara tsakanin babban ɗan yatsan kafarta da mabiyinsa, da sauran yatsun har zuwa kan ɗan ƙuri.

Ita dai irin wannan macen an ce tana da  matuƙar juriyar tarawa kuma tana da ɗan karen dadi.

Har ma Malaman Fiqhu suna cewa da so samu ne da sai a yi kari a cikin sadakinta (wato a bambanta shi da na sauran mata.)

Kammalawa

A nan zan dasa aya a cikin maudu'in nan namu na yau. Mun tattauna ne akan yadda ake gane mace daɗi. Ina fatan za ku yi amfani da ilimin da kuka samu ta siga mai kyau.

Gargaɗi: ko ƙaɗan ba zan ɗauki nauyin kaina na ɗauki na wani ba, wallahi duk wanda ya yi zina Allah sai ya ƙona shi. Kuma ko bayan ya mutu, sai ƴaƴansa sun yi zinace-zinace. 

Domin malamai sun ce zina bashi ce. Yau, mun shigo zamanin da wanda bau taɓa zinar ba ma yi ake yi da ƴaƴansa, ina ga wanda ya yi ta

Ƴan'uwa mu kiyaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post