500 Hausa Proverbs (Karin Magana 500 Na Hausa)

Hausa Proverbs
Hausa Proverbs

Ina mai yi muku maraba da zuwa shafin nan mai albarka wato Go To School. Yau, na tatttaro jerin karin magana ɗaiɗai har guda 500 na kawo muku.

Haƙiƙa Hausa sai ɗan Hausa, saboda haka sai mu tsunduma ciki kawai!

1). A saka a baka, ya fi a rataya

2). A tambayi kaza hanyar rafi? A tambayi agwagwa a sha labari

3). Abokin kuka, ba a ɓoye masa mutuwa

4). Alamar ƙarfi, tana ga mai ƙiba

5). Albasa bata yi halin ruwa ba

6). Allah ya tsari gatari da saran shuka

7). An yi ba a yi ba, an rufe ƙofa da ɓarawo

8). An yi ba a yi ba, shuka a idon makwarwa

9). Ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa

10). Ciki ba don Tuwo kaɗai aka yi shi ba

11). Ba da ni ba! Gaɗa a makwantai

12). Ba girin-girin ba, ta yi mai

13). Baki da gashin wance, ba kya yi kitson wance ba

14). Bakinka, ya tsuliyarka

15). Bishiyar giginya, na nesa ka sha inuwarki

16). Ciki da gaskiya, wuƙa ba ta huda shi

17). Ciwon ƴa mace na ƴa mace ne

18). Da rarrafe, yaro kan tashi

19). Da rashin kira, karen bebe ya ɓata

20). Da rashin tayi, akan bar arha

21). Da walakin, goro a miya

22). Daki-bari.

23). Dare, mahutar bawa.

24). Duk girman ɗantsako, ƙwai ya fi shi

25). Duk wanda ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa

26). Duk wanda ya ƙona rumbunsa, ya san inda toka take tsada

27). Kasada! Auren bashi

28). Faɗan gwaggo a kofa

29). Ga maciji ana bin ja

60). Gani, ya kori ji

31). Gaskiya ɗaci gareta

32). Gutun gatarinka, ya fi sari ka bani

33). Haihuwa fari, horon gindi

34). Hauka da naɗi, ɗanwake ya ga tubani

35). Idan ana ta ɓarawo, to a yi ta mabi sawu

36). Idan ka ga tsohuwa tana rawa a kasuwa, to ta daɗe tana yi

37). Idan ka je gari ka kowa da jela, kai ma nemi ko tsumma ne ka ɗaura

38). Idan kunne ya ji, jiki ya tsira

39). Idan makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka dutse

40). Ina raba ka da yin kiwo, kana kyalla ta haihu

41). Idan ɓera da sata, to daddawa ma da wari

42). Ihunka na jiyo

43). Jiki bai fi jiki ba

44). Jiki magayi!

45). Kafin ka ga biri, biri ya ganka

46). Kai ka faɗa? Uwar sarki a kan doki

47). Kamar da gaske, karuwa ta ga noman ɗankoli

48). Kar dai kaza ta tono wuƙar yanka ta

49). Komai nisan dare, gari zai waye

50). Komai nisan jifa, ƙasa zai faɗo

51). Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

52). Kowa ya ga balbela, da farinta ya ganta

53). Kowane tsuntsu, kukan gidansu yake yi

54). Kura ta san gidan mai babban sanda

55). Lumbu-lumbu, wutar ƙaiƙayi

56). Mahaukaciyar kasuwa, sa gabanki inda ki ke so

57). Mai guri ya zo, mai tabarma ya naɗe

58). Mai haƙuri, yakan dafa dutse ya sha romonsa

59). Mai ɗaki, shi ya san inda yake yi masa yoyo

60). Ma raina kaɗan, zai haƙura da babu

61). Matar mutum, ƙabarinsa

62). Matar shige bata daraja

63). Mu gani a ƙasa, an ce da kare ana biki a gidan su kura

64). Murucin kan hanya/dutse, baka fito ba sai da ka shirya

65). Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo

66). Nesa, ta zo kusa

67). Ni ya kai, kai ya ni

68). Ƙarya fure take, bata ƴaƴa

69). Ƙofar Allah, ta fi ta cali

70). Ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki

71). Ramin ƙarya, ƙurarre ne

72). Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya

73). Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya

74). Ranar wanka, ba a ɓoyon cibi

75). Ruwa ba sa'an Kwando ba ne

76). Ruwa ba ya tsami banza

77). Sa toka sa katsi

78). Sabon shiga, ɓarawo da sallama

79). Sai bango ya tsage, ƙadangare yake samun wajen shiga

80). Saki reshe, kama ganye

81). Sammakon bubuƙuwa

82). Samun duniyar ɗantsako

83). Samun na same ka

84). Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba

85). Sara da sassaƙa, basa hana ganji toho

86). Shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne

87). Talaka baya tashin talaka, sai tashin talaka ya zo

88). Tsautsayin takaba, auren shiɗaɗɗe

89). Tsuntsu duka tsuntsu ne

90). Tura ta kai bango

91). Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho

92). Wane kare ne ba bare ba?

93). Wayo, ya san na ƙi

94). Wayon a ci, an kori kare daga gindin ɗinya

95). Yaro bari murna, karenka ya kama zaki

96). Yaya gara takan yi da dutse? Sai kallo

97). Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi

98). A tambayi kalwa zaƙin miya? A tambayi barkono a sha labari

99). Abokin damo, guza

100). Abokin ɓarawo, ɓarawo ne

101). Abun kiriki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake yi

102). Aikin da babu lada, a bari a jingine shi

103). Allah a baki, amma a zuci sheɗan

104). Allah ɗaya, gari banban

105). Allah ya maida ƙoƙo masaki

106). Allura, ta tono garma

107). An san da wuyan biri, ake ɗaure shi a ƙugu

108). An yi gudun gara, an faɗa gidan zago

109). An yi min sagegeduwa

110). Ba a aikin banza a Kano

111). Ba a raba harshe da haƙori

112). Ba wahalalle, sai mai kwaɗayi

113). Ba wan, ba ƙanin

114). Babu maraya, sai rago

115). Bashi ga tsuntsu, ba shi ga tarko

116). Biri, tumakan banza

117).Buƙatar maje hajji, sallah

118). Da safe, ake kama fara

119). Da zafi-zafi, akan daki ƙarfe

120). Daga ganin sarkin fawa, sai miya ta yi zaƙi

121). Dalili, mai sa a leƙa gindin surika

122). Dodo ɗaya ake yiwa tsafi

123). Dogo da hankali, da ce ne

124). Duk gautar, ja ce/Kowace gauta ja ce

125). Duk kanwar, ja ce

126). Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, to ya kwana bai yi barci ba

127). Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari, riƙe masa ƙota

128). Duk wanda ya sayi rariya, ya san za ta zubar da ruwa

129). Duk wanda ya sayi tsintsiya, yasan za ta yi shara

130). Duk wanda ya ɗebo da zafi, bakinsa

131). Duk ɗan da ya hana uwarsa barci, to shima bai runtsa ba

132). Fankan-fayau

133). Fitar barden guza

134). Ga zara ga wata

135). Garin gyaran gira, an tsole idanu

136). Goɗiyar sanƙira, a hauki a riga ki tashi

137). Haihuwar guzuma, ƴa kwance uwa kwance

138). Hali, abokin tafiya

139). Hali, zanen dutse

140). Hamburin hangun/hamburin hayam

141). Hana wani, hana kai

142). Holoƙo, hadarin kaka

143). Idan juninka sammako, to wani a tafe ya kwana

144). Idan maraya ya ji ana yiwa mai uwa faɗa, sai ya kasa kunne

145). Idan rana ta fito, tafin hannu bai iya kare ta

146). Idan wani ya taka rawa aka bashi kuɗi, in wani ya taka duka zai sha

147). Ikon Allah, sai kallo

148). In da rai, da rabo

149). In ta yi ruwa, rijiya in bata yi ba masai

150). In za ka faɗi, faɗi gaskiya komai ta ja maka ka biya

151). In za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere

152). Ina ruwan biri da gada

153). Iya ruwa, fidda kai

154). Jifan gafiyar ɓaidu

155). Kafi mai kora shafawa

156). Kainuwa dashen Allah

157). Kallo hadarin nesa, ya sa an yi wanka da kashi

158). Kallon hadarin kaji

159). Kanwa uwar gami

160). Kere na yawo, zabo na yawo, wata rana za a haɗu

161). Kowa ya ci da mai, kuɗinsa

161). Kowa ya ci ladan kuturu, zai yi masa susa

162). Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha

163). Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

164). Kowa ya tuna bara, bai ji daɗin bana ba.

165). Kowace ƙwarya, da abokin burminta

167). Kulɓa na ɓarna, ana cewa jaɓa ce.

168). Kura, ga kwaɗayi ga tsoro

169). Kura, ga tsoro ga ban tsoro

170. Laifin yaro ƙiwa, laifin babba rowa

171) Lauje, cikin naɗi

172). Mai rabon ganin baɗi ko ana daka wa a turmi sai ya gani

173). Mai tarkon tsuntsaye, baya ɗaga kara

174). Mai tsoron ta mutu, shi yake maho

175). Ƙaiƙayi, koma kan masheƙiya

176). Ƙuda, wajen kwaɓayi akan mutu

177). Ƙwarya, ta bi ƙwarya

178). Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare ya yi hankali

179). Ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba

180). Sai an gwada, akan san na ƙwarai

181). Sata gidan ɓarawo, rance

182). Shege, ka fasa.Ta fi nono, fari

183). Ta nan muka faro, kuturu ya ga mai ƙyasbi

184). Takunkumi, ya fi ƙarfin bakin kaza

185). Tuna baya, shi ne roƙo

186). Wake ɗaya, shi ke ɓata gari

187). Ya daɓa wuƙa a cikinsa/ya daɓawa cikinsa wuƙa

188). Ya ɗebo ruwan, dafa kansa

189). Ya yi amai, ya lashe

190). Zafin nema, baya kawo samu

191). Zakara, bada ƙwaya ka ci tsakuwa

192). Zakaranka, raƙuminka

193.) Zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai

194). Zuma, ga zaƙi ga harbi

195). Zuru, ta ishi ɗan kunya

196). A cikin ido, ake tsawirya

197). A yarda ƙullon mangwaro, a huta da ƙuda

198). Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba

200). Abin da yawa, mutuwa ta je kasuwa

201). Abin kasuwa, na mai ciniki ne

202). Akuya, bata gasa da kura

203). Albarkacin kaza, ƙadangare ka sha ruwan kasko

204). Ashe ana tsoron inna? In ji 'ya'yan mayya

205). Ba a fafe gora, ranar tafiya

206). Ba a haɗa gudu, da susar ɗuwawu

207). Ba ka cin rama, sai 'yaryaɗi

208). Bakin rijiya, ba wajen wasan makaho ba ne

209). Bakina, ƙanin ƙafata

210). Bani in baka, shi ne tanka

211). Banza girman mahaukaci, ƙaramin mai wayo ya fi shi

212). Banza, ta kori wofi

213). Baya, ba zane

214). Bikin Magaji, baya hana na Magajiya

215). Biyu, tafi ɗaya ko a rabon ɗauki

216). Ci naka in ci nawa, ba rowa ba ce

217). Ciki, mai manta kyautar jiya

218). Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne

219). Da haihuwar yuyuyu, gwara/gara/ƙwara ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara

220). Da me, kurna ta fi magarya?

221). Da muguwar rawa, gwanda/gwamma ƙin tashi

222). Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi

223). Duba mini hanya, makaho ya so tsegumi

224). Farar aniya, laya

225). Gajen haƙuri, shi ke kawo me aka shuka

226). Garin masoyi, ba shi da nisa

227). Ginshiƙin dutse, kowa ya yi karo da kai shi ka faɗi

228). Girma da arziƙi, ita ke sa a ja sa da abawa

229). Gobe ma, rana ce

230). Gwano, baya jin warin jikinsa

231). Hadarin ƙasa, maganin mai kabido

232). Hanci, bai san daɗin gishiri ba

233). Hangen Dala, ba shiga birni ba

234). Idan amarya bata hau doki ba, ai ko ba a ɗora mata kaya ba

235). Idan mutum ya yi nisa, baya jin kira

236). Idan ɗan kaciya bai ci kaza ba, ai ba ya yi bara ba

237). Ido ba mudu ba, ya san kima/ƙima

238). In dama ta ƙiya, sai a koma hagu

239). In ka ji ana raka ni kashi, ba zawayi/zawo ba ne

240). In ta bi daga-daga, na ƙurya ka sha kashi

241). Ina ruwan bebe da harara

242). Inda jahilci ya yi kauci, sakarci ne ya zo zai nuna ilimi

243). Jaki, yana dukan taiki

244). Wutsiyar raƙumi, ta yi nesa da ƙasa/raɓa

245). Jiya, ta fi yau/ Da me, jiya ta fi yau

246). Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta

247). Kai mai kashe maciji, sai ka yi niyya ka ɗauki sanda

248). Kaska raɓi mai jini, ki bar shi da gashi

249). Kasuwa, a kai miki/maki dole

250). Kasuwa, akwashin Allah

251). Kaɗan, mai ban haushi

252). Kaza mai ƴaƴa, ita ke gudun shaho/shirwa

253). Kazar kwanci, ƙirjinki ya saba da danna

254). Kifin fadama, baya gasa da na kogi

255). Kowa ya bar gida, gida ya bar shi

256). Kowa ya ɗora miya, sai ya nemo abun kaɗi

247). Kyawun ɗan ƙwarai, ya gaji ubansa

258). Magana, jari ce

259). Maganin kar a yi, kar a soma

260). Mai zuciya ake gayawa biki, ba mai dukiya ba

261). Mai zuma ya zo, mai maɗi sai ya naɗe tabarmarsa

262). Masallacin kura, ba a baiwa kare limanci

263). Masallacin kura, mai yawan ƙasusuwa

264). Maza, dangin gurjiya sai an fasa akan san bidi

265). Meye gamin kifi da kaska?

266). Na Allah, baya ƙarewa

267). Na zangi, moriyarka da nisa

268). Na zaune, bai ga gari ba

269). Nan gani nan bari, farar tumfafiya

270). Ƙadangaren bakin tulu, a karka a kar tulu, a bar ka ka ɓata ruwa

271). Ƙarfe duka ƙarfe ne, amma a cikin ƙarafa akwai zinari da azurfa

272). Ƙasar kago, ta mai da kago ce

273). Rigakafi, ya fi magani

274). Rumbun ƙasa, a tashi a barka

275). Saki reshe, ka kama ganye

276). Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya miƙa kai ya yi kallo

277). Shirim, ba inuwa

278). Sun fi kusa, Auyo da Haɗeja

279). Ta fari, ta rago

280). Ta faru ta ƙare, an yiwa mai dami ɗaya sata

281). Ta leƙo, ta koma

282). Taron na ayya, gayyar banza

283). Tashi da wuri, shi kan hana gira toho

284). Taura biyu, basa taunuwa a baki ɗaya

285). Tsiga tsiyau, kazar matsiyaci

286). Tsugunne, bata ƙare ba

287). Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farin gashinta

288). Wanda bai san Allah ba, sai wuta ta ƙona shi

289). Ɗan kuka, mai jawo wa uwarsa jifa

290). Ɗinyar makaho, ta nuna a hannunsa

291). Ya ɓace ɓat, kamar ɓatan dabo

292). Yabon kai, jahilci ne

293). Yanzu-yanzu, sai Allah

294). Yautai mugun tsuntsu, masha miyarka sai ya yi dare

295). Yaɗin mage, kowa ya ci ka sai ya yi amai

296). Zaman duniya, iyawa ne

297). 'Yar bori, ba ta kallon bori

298). Abincin wani, gubar wani

299). Aikin banza, harara a duhu

300). Aikin banza, shafa lalle a ɗuwawu.

301). Aikin banza, tura agwagwa cikin ruwa

302). Allah ga mu gare ka, bawan sarki ya rasa doki

303). Ba a baki na ba, an ce banten sarki ya jirge

304). Ba a hana ma bada rago, fata

305). Ba a sake wa tuwo, suna

306). Ba don mahauci ba, da mai taro bai ci naman saniya ba

307). Bakin Rijiya, ba wajen wasan yara ba ne

308). Ban ci kasuwa ba, rumfa bata faɗa min ba

309). Ban gane ba, an yi yamma da kare

310). Baƙar fura, ana gama ki mai gida na mutuwa

311). Bin umarni, waiwayen makaho

312). Biri da gatari, hasarar mai gona

313). Da alheri, uwar kishiya ta hau kura

314). Da kamar wuya, a dafa kaza a jefar

315). Da na sani, ƙeya ce

316). Da ruwan ciki, ake jan na rijiya

317). Don tuwon gobe, ake wanke tunkunya

318). Duk wanda ya ce bai iya kuka ba, uwarsa ce bata mutu ba

319). Duk wanda ya ce garinsu da nisa, ba a kama shi ya kuɓu ce ba

320). Farilla, tusa a cikin barci

321). Farin cikin ɓarawo, ya taras da ƙofa buɗe

322). Fuska, ita ke sayar da riga

323). Gaɗar giwa, toro ke buga ganga

324). Ikon Allah, kare da tallan tsire

325). Ina sane, karuwa ta taka matar aure

326). Jiya ba yau ba, in ji tsohuwa ta ga kuɗin tsarince

327). Jure fari, na mai akuya ne

328). Kafin a yi ɗaran, aka yi kwanɗi

329). Karambanin akuya, ya saka ta leƙa ɗakin kura

330). Kayan amale, ya fi ƙarfin jaki

331). Ko biri ya karye, sai ya hau runhu

332). Komai baƙin cikin ɗan tsako, ba zai ci ɗan shirwa ba

333). Raƙumi uban gararanba, kowa ya sake ka sai ya nemo ka.

334). Kura-ta-ci-kure

335). Kyawun saurayi, ya auri budurwa

336). Lange-lange, mai ramar ƙeta

337). Mai bunu a gindi, baya kai gudunmawar gobara

338). Mai rawar kai, baya ɗigirgire

339). Mai tsoron ta mutu, shi yake maho

340). Me na sama ya ci, balle ya baiwa na ƙasa

341). Me za a fasa? Mutuwa ko hisabi?

342). Mu je zuwa, mahaukaci ya hau kura

343). Mutu ka raba, takalmin kaza

344). Naman da ya fi kusa da wuta, shi ya fi saurin gasuwa

345). Nesa-nesa, kallon kurar Jatau

346). Nono ya sake hali, mage ta sha tinya

347). Ƙawancen gaskiya, a yi shi da wando

348). Ƙazantar da ba a gani ba, sunanta tsafta

349). Ragamar damisa, a jaki da nisa

350). Randar cikin ɗaka, Allah ke ba ki ruwa

351). Rashin jini, rashin tsagawa

352). Rashin mutunci biki ne, kowa ya yi maka ka rama masa

353). Rikicin duniya, da mai rai ake yi

354). Ruwan kashe gobara, ba zaɓi

355). Sabon salo, gemu a kafaɗa

356). Sakarci, dukan kura da gwado

357). Sakarci, jiran jirgi a tashar mota

358). Sakarci, tura agwagwa a ruwa

359). Sandar dukan gurgu, yana kallo ake saro ta

360). Sani asali, shi saka kare cin alli

361). Saniyar da ba ta da jela, Allah ke kore mata ƙuda

362). Sara ɗaya, shi ke da bishiya

363). Shegen sama, kura tahangi biri

364). Tafiya ta tashi, ƙuad ya ga mai tallen tsire

365). Tashin hankali, ba a sa maka rana

366). Tsautsayin tauna, maye ya ci jariri

367). Tsohuwar mota, ga shan mai ga aiki

368). Tsugunne ba ta ƙare ba, an sayar da kare an sayi mage

369). Tunku, ya san jiɓar da ya ke yi wa kashi

370). Tuntuɓe, daɗin gushi

371). Turancin ungulu, sai sarkin fawa

372). Tusa, ba ta hura wuta

373). Umma, umma biyu, ta fi umma ɗaya

374). Ungulu, ba kazar kowa ba ce

375). Ungulu, ta koma gidanta na tsamiya

376). Walbisi, in ji kare da ya taka sisi

377). Wanda ba shi da doki, ba ya ƙyamar jaki

378). Wanda bai nom aba, ba ya ƙyamar awo

379). Wanda ya ci da kansa, shi ne sarkin noma

380). Wawa ana sonka, amma ba a son haihuwar ka

381). Wawa, dariyarka abin da dariya

382). Ɗan agola, mai wuyar ban nama

383). Ɗan maciji ya fi ɗan kura tsiya

384). Ɗiɗiricin balaga, kiran miji da akaifa

385). Yau da gobe karyar Allah, komai gudun mutum ta kamo shi

386). Yau da kallo, gobe da labari

387). Yawan shekaru, ba shi ne wayo ba

388). Zubar da miyau, masomin hauka

389). Zubar da yawu, masomin hauka

390). Zuma, sai da wuta

391). A rina, an saci zanen mahaukaciya

392). A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye

393). Abun dariya, kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa

394). Allah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida

395). Allah, ya kawo baƙon da zai ci da ɗan gari

396). Amfanin zunubi, romo

397). An ce da ido wa ka raina? Ya ce wanda na ke gani yau da kullum

398). Ana bikin duniya, ake na kiyama

399). Ba cas, ba as

400). Babban goro, sai magogin ƙarfe.

401). Bakin da Allah ya tsaga, ba zai hana shi abinci ba

402). Ban ci nanin ba, nanin ba za ta ci ni ba

403). Ban ga ta zama ba, an saci ɗan ɓarawo

404). Ban sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya

405). Baya ganin zalau, sai ya leƙa

406). Cikina kwarkwaro, cikina tashiya

407). Cil-da-cil, ganin annabin tsohuwa

408). Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa

409). Da mai kama, ake ƙota

410). Da sauran rina, a kaba

411). Da wuya ta kashe ka, gwara/gwanda daɗi ya kashe

412). Duk wanda ya samu rana, sai ya yi shanya

413). Duniya, rawar 'yammata na gaba ya koma baya

414). Fankam-fankam, bata kilishi

415). Faɗan da ya fi ƙarfinka, mai da shi wasa

416). Ga bikin zuwa, babu zani

417). Ga fili, ga mai doki

418). Gaba tsini, baya siyaki

419). Gaba ta kai ni, gobarar titi

420). Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah

421). Garaje, ga dami

422). Guntun goro, ya fi babban dutse

423). Gurin da ba ƙasa, nan ake gardamar kokawa

424). Haka ma arziƙi ne, ka yi baƙo ya kashe ka

425). Idan ba a yi sharar masallaci ba, a yi ta kasuwa

426). Idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa

427). Idan ka ga mutum yana shinshina/sinsina takalami, so yake ya ɗauka

428). Idan mafaɗin magana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne

429). Idan maye ya manta, uwar ɗiya bata manta

430). Idan tururuwa ta so lalacewa, sai ta fara gashi

431). Ihunka, banza

432). Ka ƙi naka dubu/duniya ta so shi

433). Kallon kitse, ake yiwa rogo

434). Karambanin baƙo, ya shiga yaƙin masu gari

435). Kare da kuɗinsa, sai ya sha lahaula

436). Karo ɗaya, ko da ƙwai da dutse a yi

437). Kasada, cinikin tsuntsu a sama

438). Kasuwar da ba a gayyace ba, daɗin ci gare ta

439). Komai aka yi da sabara, sai ta yi kere

440). Kuturu da kuɗinsa, al-kaki sai na ƙasan langa

441). Kwaɗayi, mabuɗin wahala

442). Kyautar shigo ɗaka, ka yi kuka

443). Kyawun ɗan maciji, banza

444). Magana, zarar bunu

445). Mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce kanku ake ji, ni wanka na na ke yi

446). Mai kamar zuwa, akan aika

447). Me ya fi lafiyata, cin tsiren mata

448). Mugun nufi, baya kashe ɗan barewa

449). Mutum baya ƙin ta mutane, an ce da ɓarawo ya gudu

450). Na yi maka ciki, na yi maka goyo!

451). Na zo kenan, zuwa sojan badaskare

452). Ƙaramar danga, daɗin tsallaka

453). Ƙuruci, dangin hauka

454). Ragon malam, ga kyau ga araha

455). Ratsa unguwa, a haifi kamarka

456). Ruwa, ya ƙarewa ɗan kada

457). Ruwan da ya buge ka/dake ka, shi ne ruwa

458). Ruwan da ya tafasa, baya tsoron ƙuna

459). Ruwan dare, gama duniya

460). Sa'a, ta fi gata

461). Sa'a, ta fi sammako

462). Sa'a, tafi manyan kaya

463). Sarki goma, zamani goma

464). Sayen biri, ba igiya

465). Shiru ka ke ji, malam ya ci shirwa

466). So, mai hana ganin laifi

467). Ta guntso, za ta fesar

468). Ta yaro, kyau take bata ƙarko

469). Tauraruwa mai wutsiya, ganinki ba alheri

470). Taɓa kiɗi, taɓa karatu

471). Tsintacciyar mage, ba ta mage

472). Tsuntsu daga sama, gasasshe

473). Tusa, ta ƙare wa bodari

474). Wanda ruwa ya ciyo shi, in aka miƙa masa takobi sai ya kama

475). Wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai yi nesa da ita

476). Wari ya ke yi, an ce da makaho ga ido

477). Wuce gona, da iri

478). Wuce makaɗi, da rawa

479). Ɗan gata, masha wuyar wata rana

480). Yaushe rabon duniya, da ayya-raye!

481). Yaro, masomin babba

482). Yunwa, ba a mata lahaula

483). Zama lafiya, ya fi zama ɗan sarki

484). Zuwa da wuri, ya fi zuwa da wuri

485). A juri kai ruwa rafi, wata rana gora zai fashe

486). A kai gwauro, a kai mari

487). Mugunta fitsarin fak’o

488). Girman kai rawanin tsiya

489). Idan ka daka rawar wani, ka rasa turmin daka taka

490). Da ruwan ciki akan ja na rijiya

491). Idan fitsari banza ne, kaza ta yi mana

492). Munafunci dodo ne, yakan ci mai shi

493). Banza ba ta kai zomo kasuwa ba

494). Allah ∂aya gari bamban

495). Abincin wani gubar wani

496). A bar kaza cikin gashinta

497). Ba a bari a kwashe duka

498). Ba a raba hanta da jini

499). Ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi

500). Da dan gari a kan ci gari

Wadannan su ne "Karin Magana na Hausa" guda dari biyar wadanda muka fada muku za mu kawo muku.

Tabbas ga dukkan alamu mun cika maganarmu.

Muna fatan nan gaba kadan za mu dada kara binciko wadansu nau'ikan karin maganar mu kara kawo su a shafin nan mai albarka.

Kammalawa

Da wannan na ke son rufe babin wannan wallafa. Sai dai zan so duk wanda ya ga wata tangarda, rubutun karin magana ba daidai ba, ko kuma ya ga gyara a ciki sai ya yi kokarin yin sharhi. Kada ku manta, ku yi share domin sauran Hausawa su amfana.

Allah ya kara wa Hausa albarka.

Post a Comment

Previous Post Next Post