Karanta Labarin Cin Durin Yar Alhaji

Wato ko, Allah dai ya kiyashe mu da aikata aikin da na sani! Aikin da mutum shi da kansa ya san ba daidai ya aikata ba.

Na rantse har da Allah ban taba tunanin asiri zai tonu ba, a yi min irin wagga wulakancin.

Tabbas, irin wulakanci da tozarcin da Alhaji Mudi ‘Dan Makole ya sa aka yi min ba lallai na taba mantawa da shi ba a rayuwa.

Farkon Labari

Zaune na ke a cikin wani jahilin cell mara dadin zama bare kuma kyaun gani, babu duniyar da na ke ciki tsulum-tsulum face duniyar Tunani.

Oh, rayuwa, wai yau ni Mado aka daure saboda kawai kutumata ta jawo min na ci durin ‘yar Alhaji?

Amma kuwa lallai in har na samu na kubuta, na shaki iskar ‘yanci, to, la shakka sai na yi wa Alhaji Mudi ‘Dan Makole abin da ba zai taba mantawa da shi ba a rayuwarsa.

Kuma abin da zai sa ya yi nadamar irin cin zarafin da ya yi min akan fatar duri.

Irin wadannan tunaninnika su na yi ta yi har dare ya raba, ga sanyi, ga sauro, ga cikin cell din nan ba wata iska mai dadi sai shegen wari kawai da ke buguna ko-ta-ko-ina.

Kafin garin Allah ya waye, azzaluman saurayen cikin cell din nan duk sun bi sun ci kutumar ubana yadda ko barci ban samu na yi ko da kai daya ba.

Kashegari na yi ta raba idanu ina sa ran ko zan ji wani ko wata daga cikin sauran dangina ya zo ko ta zo belina, amma shiru ka ke ji kai ka ce shaho ne ya ci shirwa.

Da gari ya ‘dan hantsa sosai, sai ga wani kofur tsudum ya fado cikin cell din da aka killace ni hannunsa dauke da takeaway. To, dama mai laifi ne aka tsare, don haka ko sallama bai yi ba.

Shege kai da ganinsa ka san imanin kansa bai wadace shi ba, bare kuma tsoron Allah.

Ya kalle ni a wulakance ya ce, “Kai ne Mado ko?”

Na dago kai na ce, “Eh, ni ne Ofisa.”

Daga haka bai kara ce min komai ba, sai ya aje takeaway din hannunsa ya fice hadi da garkamo kofa.

Wata zuciyar ta shawarce ni da, “Kada na ci abincin nan…” wata kuwa ta ce min, “Uhm uhm Mado, kada ka yi wa kanka ragon shiri, ga dukkan alamu za ka jima a wurin nan.

Ci yanzu dai tukun, kana sai ka zuba wa ikon Ubangiji ido daga baya.”

Na dauki shawara ta biyu. Nan na jawo takeaway din nan, na bude shi na far masa da ci. Kan ai-haka ai-haka na mika shi cikin zarmemen cikina.

Duk da ban koshi ba, sai da na yi wata ‘yar autar gyatsa sannan na tande hannuna hadi da goge bakina yadda ko kaza ce da kanta ta zo ta ganni a wannan lokacin ba za ta yarda na ci wani abu wai shi abinci ba.

Shi ko fankon takeaway din nan, ban yi wata-wata ba sai na dauke shi, na mike tsaye tsam na je ta taga na tukunkune shi na wurga shege waje.

Na dawo inda na ke da a zaune, na kara share waje na zauna na yi kurum.

Ko da dare ya yi ‘yan kaniyar kwalawan nan ba su bar ni na yi barci lafiya ba, sai da wasu mutum biyu suka zo suka ragargajeni yadda ya kamata.

Ni kaina da na ji dukan ya kai duka, ban ma san na takarkare na kirba wa daya daga cikinsu naushi ba wadda saboda tsabar nausuwar da ya yi da kyar ya fice daga cell din, dayan ma da ya ga wancan ya sulale shi ma sai ya bi bayansa.

A haka dai na samu wuri a cikin cell din na rakabe, ina mammatsa duk inda ke min ciwo a jikina, domin na daku kwarai da gaske.

Abinda ya Faru

Sai bayan kashegarin ranar da su ka yi min shegen dukan nan suka sakeni, ba tare da kowa ya zo belina ba.

Da har na yi niyyar wucewa gida, sai kuma wani abu ya fado min a raina, “Ni dai na san haka kurum wadannan kwalawa ba za su zo su ragargajeni ba, dole akwai wanda ya sa su duk da na san Alhaji Mudi ne zai aikata hakan amma dai ina so na ji tabbas ne.”

Zamana na yi a kofar station din har wajejen karfe biyu cikin ‘yan sandan nan, ban tafi gida ba.

Can wajen karfe uku sai ga daya daga cikin wadanda suka sauke gajiyarsu a kaina jiya ya iso, ko da ya kyalla ido ya ganni, sai ya tuntsire da dariya yace, “To, kai Mudi me ka ke yi har yanzu a wurin nan? Ina ai Alhaji ya sa an yi maka abin da ya ke ganin ya dace da kai!”

Da na kada baki sai na ce masa, “Ba komai, kawai shan iska na ke yi kafin na kara wa mota ta mai.”

Nan ya zauna, mu ka dan fara hira, har ya ke fada min ai Alhaji Mudi ne ya basu dubu talatin na ajiyeni kwana biyu da suka yi, ya kuma umarcesu jiya da su ragargajeni kafin su sakeni yau.

Da na ji haka sai na tabbatar da na samu wanda na ke nema, don haka bayan la’asar sai na tattara i-nawa-i-inawa na nufi gida.

Dawowa ta Gida

Wato sai da na je station din nan aka ci ubana sannan na kara tabbatarwa da kaina ni ba kowa ba ne, ba kuma kowan kowa ba ne.

Bayan na dawo gida na samu kamar sati uku, na ‘dan wawwarke, na murmuro, sai kuma maganar fansar da zan dauka a kan Alhaji mudi ta fado mini a raina.

Amma kafin mu je ga kan fansar sai na fara da baku labarin abin da ya hada har Alhaji Mudi ya sa ‘yan sanda suka yi ram da ni har na kwana biyu a wurinsu.

Asalin Rigimar

Duk irin azabar da na sha a hannun kwalawan nan ba komai ne ya jawo mini ba face kutumata wacce na kasa sarrafawa.

Kuma in har zan dora wa wani alhaki, to, gaskiya ba na tunanin zan tsallake dadin durin ya sa ni cikin wannan mawuyacin hali.

A nan zan dasa aya a kashi na farko na dogon labarin nan, in har kun fara ‘dan jin dadin labarin, to, zan so ku yi sharhi sannan ku yi share na wannan labarin domin mu cigaba.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts