Yadda Ake Yiwa Mace Ciki

Maudu’in da za mu tattauna akansa yau shi ne yi wa mace ciki.

Dalilin da yasa za mu tattauna akansa saboda mutane da dama na yin tambayoyi masu tarin yawa game da shi a manema ta Google.

Zaman al’ummar Hausa wani irin zama ne wanda akwai abubuwan ilimi da dama wadanda ba a fitowa fili a na yi wa mutane bayani a kansu.

In har ka fito, ka na bayani a kansu, kai tsaye wasu [baragurbin] za su fara jifanka da munanan kalamai.

Kuma a zahirin gaskiya, irin wadannan maudu’ai ya zama wajibia tattauna a kansu domin samu a wayar wa da wadanda basu sani ba kai.

Shin Menene Juna Biyu (Ciki)

Ciki, ciki, da ciki kalmomi ne guda uku mabambanta. Kowacce kalma daga cikinsu na kunshe da tata ma’anar.

 • Ciki (Juna Biyu): shi ne wanda mace ke dauka yayin da namiji ya sadu da ita [walau mijin sunna ko akasin haka].
 • Ciki (Asalin Rumbun Ciki): shi ne wanda kowanne ‘dan Adam ke dauke da shi, a cikinsa ne mafi akasarin makasudan sarrafa gangar jikin ‘dan Adam su ke.”

In ba zan manta ba, akwai karin magana masu tarin yawa game da ciki.

Daga cikinsu akwai:

 1. Ciki dan uwan kwarya ne, sai da dauraya
 2. Ciki ba don Tuwo kadai aka yi shi ba
 3. Ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi
 4. Ya daba wuka a cikinsa
 5. Ciki, mai manta kyautar jiya
 6. Da ruwan ciki, ake jan na rijiya
 7. Cikina kwarkwaro, cikina tashiya
 8. Na yi maka ciki, na yi maka goyo

Kadan kenan daga cikin karin magana wadanda ke da alaka da ciki.

 • Ciki: kalma ce da ake amfani da ita domin zayyana cikin wani abu lo da ke cikin wani abj.

Misali:

 1. Na shiga cikin daki na
 2. Za ku same shi a ciki
 3. A ciki na koro shi
 4. Daga ciki mu ka shiga

Mun yi wannan warwararren bayani domin samun damar dasa wa maudu’inmu tushe mai kyau wanda duk rashin fahimtar mutum zai fahimta.

Ta Yaya Ake Samun Ciki

Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi wajen samun ciki. Wasu daga cikin kun san su. Wasu kuma ba lallai kun san su ba.

Daga ciki akwai:

1. Samun Ciki ta Hanyar Tarawa

Yayin da mace da namiji su ka tara ba tare da yin amfani da kwaroron roba ba, kuma har namijin ya tsiyaya ruwan maniyyinsa cikin mahaifar mace, to za ta iya daukar ciki.

Sai dai shi kansa samun cikin ba ya yiwuwa sai in har namijin lafiya kalau ya ke.

In kuwa ya kasance namijin yana da matsalar tsinkewar mani, ko wata lalurar da ke hana ‘da namiji yi wa mace ciki, to, ko ya tara da ita ba za ta dauki ciki ba.

2. Samun Ciki ta Hanyar Allura

A kasashen da aka ci gaba, kai har ma da kasarmu Najeriya, akwai wurin da ake yi wa mace allurar ciki kuma ta dau juna biyu ba tare da ta tara da namiji ba.

Ita dai wannan allura yadda ake yinta shi ne; likitoci za su karbi maniyyyin namiji, sai su karbi na mace, sannan su zuke kwayoyin halittar cikinsa a alura.

Daga nan, sai su yi wa mace allurar kwayoyin halittar kai tsaye zuwa cikin mahaifarta.

Hanyar da suke bi wajen karbar samun din maniyyin su ne; mace za ta yi wani abu wanda zai sa ta kawo kai sai ta saka manin a kwalba.

Shi ma namijin haka zai yi, sai ya saka manin a cikin kwalba.

3. Samun Ciki da Rainonsa da Inji

Shin ko kun san cewa yanzu haka an samu fasahar da ake iya rainon ciki da inji har yakai munzalin haihuwa ba tare da yana cikin uwarsa ba?

Ita dai wannan hanyar, likitoci na amfani da maniyyin namiji ne da mace sai su zuke kwayoyon halittar su gauraya su.

Sannan su saka su a mahaifar inji, inda cikin zai fara girma, yana sauya halitta har ya kai munzalin haihuwa.

Rufewa

Wadannan su ne kadan daga cikin hanyoyin da ake samun ciki, har wani lokacin ma a rene shi. Mun yi wannan bayani ne domin ci gaba da gina ginshikin maudu’inmu.

Yadda Ake Yi Wa Mace Ciki

Duk wani namiji ko mace ya sani, kuma ta san yadda ake yi wa mace ciki. Ana samun ciki ne ta hanyar tarawa.

Kuma lokuta da dama ana samunsa bisa kuskure, wato ta hanyar zina.

Yayin da cikin da aka fi maraba da shi shine wanda aka samu ta hanyar aure.

Mazinata har ma da masu aure in ba sa son mace ta dauki ciki, to suna amfani da kwaroron roba ne wanda namiji ke sawa.

Sai dai akwai bayanan da suka tabbatar da cewa mata ma akwai irin nasu samfur din kwaroron robar.

Duk da haka, ba kowacce mace ce ta damu da amfani da shi ba saboda maza na sawa.

Mu dai du’a’inmu kullum shi ne: Allah ka raba mu da aikata zina, ka raba mu da kawo shege duniya. Ka kuma raba mu da duk wasu nau’ika na aikin masha’a.

Kammalawa

Bayin Allah, a nan za mu dasa aya a cikin maudu’inmu na yau akan yadda ake yi wa mace ciki.

Bayanin na da mu ka yi, mun yi shi ne domin ilimantarwa ba tare da wata mummunar niyya ba ta shayar da mutane guba a matsayin ilimi.

Kada ku manta, ku yi sharhi in har kuna da tambayoyin da kuke son a amsa muku.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts